Nigerian news All categories All tags
Za a saki sunayen wasu Ministoci da Gwamnoni da Sanatocin da su ka saci kudin Najeriya

Za a saki sunayen wasu Ministoci da Gwamnoni da Sanatocin da su ka saci kudin Najeriya

- Gwamnatin Shugaba Buhari za ta fito da sunayen ragowar barayin Najeriya

- A baya an fito da jerin mutane kusan 30 da su ka handame dukiyar jama’a

- Har yanzu akwai mutane sama da 20 da ba a kawo sunan su ba a cikin jerin

Mun samu labari cewa nan ba da dadewa ba ne Gwamnatin Shugaba Buhari za ta saki sunayen wasu Ministoci da tsofaffin Gwamnoni da kuma Sanatocin kasar nan da su ka saci kudin Najeriya.

Za a saki sunayen wasu Ministoci da Gwamnoni da Sanatocin da su ka saci kudin Najeriya

Za a kara saki sunayen wadanda su ka wawure dukiyar jama’a

Jaridar Punch ta rahoto cewa akwai yiwuwar a fito da wani sabon jeri na wadanda ake zargi da laifin wawure dukiyar al’umma. Wannan karo za a samu tsofaffin Gwamnoni da manyan ‘Yan Majalisu da Ministocin kasar.

KU KARANTA: Jihohin da su ka fi samun kudin shiga a Najeriya

A wannan jerin da za a fito da shi, za a kawo wadanda ba a ma taba zargin su ko maka su Kotu da laifin sata ba. A baya dai an fito da sunayen mutane 29 cikin akalla 55 da ake zargi sun saci makudan kudi a lokacin PDP.

Wata majiyar mu a fadar Shugaban kasa ta bayyana mana cewa ana sa rai Ministan yada labarai watau Lai Mohammed ya saki wasu sunaye dabam na barayi. Dama dai fadar Shugaban kasar tace akwai wadanda ba a kawo sunan su ba

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel