Nigerian news All categories All tags
Jam'iyyar APC reshen jihar Edo ta tubure akan tsawaita wa'adin Oyegun

Jam'iyyar APC reshen jihar Edo ta tubure akan tsawaita wa'adin Oyegun

A yayin da kakakin jam'iyyar APC na kasa Timi Frank ya yi ikirarin cewa, a halin yanzu ma su neman a tsawaita wa'adin shugaban jam'iyyar Cif John Odigie-Oyegun a kujerar sa su ne makiyan jam'iyyar na hakika da ko shakka ba bu.

Jaridar The Punch ta ruwiato cewa, kimanin gwamnoni 24 na jam'iyyar su na goyon bayan tsawaita wa'adin shugaban jam'iyyar har zuwa shekara guda, sai dai wasu daga cikin gwamnoni irin su Nasir El-Rufa'i na jihar Kaduna da takwaran sa na jihar Kogi sun juya baya akan wannan bukata.

Jam'iyyar APC reshen jihar Edo ta tubure akan tsawaita wa'adin Oyegun

Jam'iyyar APC reshen jihar Edo ta tubure akan tsawaita wa'adin Oyegun

A yayin haka kuma, reshen jam'iyyar na jihar Edo wadda ita ce mahaifar shugaban jam'iyyar ta juya bayan ta akan yunkuri na mafi akasarin gwamnonin jam'iyyar dangane da tsawaita wa'adin sa a kujerar.

KARANTA KUMA: Dalibai a jihar Adamawa sun yi shirin kawo karshen rikicin Arewa maso Gabashin Najeriya

Da yake ganawa da manema labarai a ranar yau ta Asabar, shugaban jam'iyyar reshen jihar Edo Mista Anslem Ojezua ya bayyana cewa, manufar gwamnonin jam'iyyar na goyon shugaban kasa Muhammadu Buhari na tsawaita wa'adin Oyegun ya sabawa matsaya ta farko da shugabannin jam'iyyar na jihohi suka dauka.

Ojezua ya kara da cewa, gwamnonin masu wannan ra'ayi sun amince da rinjayen hujjar shugaba Buhari a madadin bin ra'ayin kawunan su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel