Nigerian news All categories All tags
Da dumi-dumi: Rundunar sojin Najeriya sun ceto mutane 149 daga hannun Boko Haram, sun damke yan ta’adda 5

Da dumi-dumi: Rundunar sojin Najeriya sun ceto mutane 149 daga hannun Boko Haram, sun damke yan ta’adda 5

Rundunar sojin Najeriya karkashin jagorancin Laftanan Janar Tukur Buratai sun ceto mutane 149 daga hannun yan ta’addan Boko Haram a mabuyarsu.

An samu wannan gagarumin nasara ne ranan Asabar, 7 ga watan Afrilu, 2018. Hukumar ta bayyana wannan ne a jawabin da kakakinta ta saki a au inda yace:

“Rundunar sojin Operation Lafiya Dole na cigaba da samun nasara wajen hako yan Boko Haram daga mabuyarsu bayan sun arce daga dajin Sambisa.

A jiya Asabar, jami’an tsaron sun karasa mabuyar Boko Haram a Yerimari Kura domin ceto wasu mutanen da suke rike dashi.

KU KARANTA: Ajimobi, Ganduje da Okorocha sun shirya tsaf domin yakin shugaban jam'iyyar APC

An wani musayan wuta da ya auku, an hallaka yan Boko Haram 3 kuma an damke 5. Jami’anmu sun ceto mata 54 da yara 95 da ke hannun yan Boko Haram din kuma an ruguza gidajensu.

Tuni an kai wadanda aka ceto asibitin 21 Brigade Medical Center domin duba su.”

Da dumi-dumi: Rundunar sojin Najeriya sun ceto mutane 149 daga hannun Boko Haram, sun damke yan ta’adda 5

Da dumi-dumi: Rundunar sojin Najeriya sun ceto mutane 149 daga hannun Boko Haram, sun damke yan ta’adda 5

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa rundunar sojin Najeriyan sun hallaka yan tada zaune tsaye 21 a jijar Zamfara bayan wani musayan wuta da akayi a makon da ya gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a: https://facebook.com/naijcomhausa https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel