Nigerian news All categories All tags
Baragurbin yan PDP ne suka koma APC – Makarfi

Baragurbin yan PDP ne suka koma APC – Makarfi

- Shirye-shiryen PDP na dawo mulki yayi nisa

- Shugaban jamiyyar ya bayyana hakan ne yayin taronsu na na motsa jam'iyya a Katsina

Tsohon shugaban jam’iyyar PDP ta kasa, Ahmed Makrafi, yace baragurbin yan jamiyyar ne da suke bata mata suna suka koma daga cikinta.

Baragurbin yan PDP ne suka koma APC – Makarfi

Ahmed Makrafi

A cewarsa, “Yanzu haka dai duk wadanda suka rage a cikin PDP mutane ne masu mutunci da kamala.”

“Ina mai tabbatar muku da cewa in dai har jam’iyyar mu ta PDP ta samu nasarar cin zaben 2019, zata mai da hankali ne wurin kyautata jin dadin al’ummar Najeriya.”

Ahmed Makarfi dai ya fadi hakan ne, a jiya Asabar yayin gudanar da gangamin taron jam’iyyar na shiyyar Arewa maso yamma da yaguna a Jihar Katsina.

KU KARANTA: Kudin da Buhari zai cire na sayen makamai ya jawo ka-ce-na-ce a Majalisa

A wurin taron ne kuma tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya bukaci yan Najeriya da su tabbata sun yi rijistar katin zabensu domin sai da shi ne zasu iya zabar wadanda suke so a kakar zabe mai zuwa ta 2019.

A don haka ne sai yayi kira ga yan jam’iyyar PDP da su kara kaimi wajen wayar da kan mutanen da shekarunsu suka kai su kada kuri’a.

Da yake magana, Uche Secondus, wanda shi ne shugaban jam’iyyar ta kasa, ya ce, yayi mutukar jin dadin yadda mutane suka yi cikar kwari domin halartar taron, bisa hakan ne ma ya yake ganin zasu iya cin zaben gwamnan jihar ta Katsina.

“Jam’iyyar PDP lallai tana da karfin da muke bukata na cin zabe a Jihar Katsina da ma kasa baki daya a 2019.” A cewar Uche Secondus.

Baragurbin yan PDP ne suka koma APC – Makarfi

Uche Secondus

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN), ya rawaito cewa wasu daga cikin yan jam’iyyar PDM da APGA da kuma APC sun sauya sheka zuwa jam’iyyar ta PDP yayin taron.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel