Nigerian news All categories All tags
Tsaffin gwamnoni 2 dake muradin kujerar shugaban jam'iyyar APC

Tsaffin gwamnoni 2 dake muradin kujerar shugaban jam'iyyar APC

A yayin da jam'iyyar APC ke tsaka cikin rikicin tsawaita wa'adin shugaban jam'iyyar Cif John Odigie-Oyegun a kan kujerar sa har na tsawon shekara guda, wasu ko sun fara bayyana kwadayin su na karbar jagoranci idan har hakan bai tabbata ba.

Wannan lamari ya sanya wasu daga cikin gwamnonin jihohin ke ta kai komo a jihohin su don ganin rashin tabbatuwar hakan na tsawaita wa'addin shugaban jam'iyyar, inda suke neman dabbaka wannan ra'ayi na su a taron shugabannin jam'iyyar da za a gudanar a ranar Litinin ta mako mai zuwa.

Shugaban jam'iyyar APC; Cif John Odigie-Oyegun

Shugaban jam'iyyar APC; Cif John Odigie-Oyegun

Legit.ng ta kawo muku jerin tsaffin gwamnonin biyu dake kan gaba cikin jeranton masu hankoron wannan kujera ta shugaban jam'iyyar APC da suka hadar da; tsohon gwamnan jihar Cross River; Cif Clement Ebri da kuma tsohon gwamnan jihar Edo; Adams Oshiomhole.

KARANTA KUMA: An yankewa wani Kare hukuncin kisa da laifin kashe Ubangidan sa

A makon da ya gabata ne jaridar Legit.ng ta kawo muku jerin mutane biyar da Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, kanwa uwar gamin matsalolin jam'iyyar ya bayyana a matsayin 'yan takarar sa na shugabancin jam'iyyar.

A yayin haka kuma, jaridar ta ruwaito cewa wasu daliban makarantun gaba da sakandire a jihar Adamawa sun bayyana ra'ayoyin su dangane da yadda za a kawo karshen tashin-tashina a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel