Nigerian news All categories All tags
Ajimobi, Ganduje da Okorocha sun shirya tsaf domin yakin shugaban jam'iyyar APC

Ajimobi, Ganduje da Okorocha sun shirya tsaf domin yakin shugaban jam'iyyar APC

Akwai alamomin masu karfin gaske dake nuna cewa, wakilan jam'iyyar APC na jihohin kasar nan sun fara karkata akalar su tare dawo rakiyar baiwa shugaban jam'iyyar na kasa karin shekara guda na wa'adi a kujera ta shugabancin jam'iyyar.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, gwamnonin jihohi sun kai ga wakilan jam'iyyar a jihohin su na neman su sauya yarjejeniyar su da shugaban kasa Muhammadu Buhari na bukatar gudanar da gangamin jam'iyyar domin aiwatar da zaben sabbin shugabannin ta.

Rahotannin sun bayyana cewa, wakilan jam'iyyar na jihohi da wasu mambobin ta tuni a yammacin ranar Juma'ar da ta gabata sun fara garzayawa birnin tarayya domin halartar taron shugabannin jam'iyyar da za a gudanar a ranar Litinin.

Gwamnonin APC yayin ziyarar shugaba Buhari a garin Daura

Gwamnonin APC yayin ziyarar shugaba Buhari a garin Daura

Legit.ng da sanadin jaridar The Punch ta kawo muku jerin gwamnoni uku da zasu daura damara ta ganin shugaban jam'iyya ya samu dama ta tsawaita wa'adin sa a kujerar shugaban jam'iyyar, inda gwamnan jihar Oyo Abiola Ajimobi, zai gana da gaba daya wakilan jam'iyyar na jihohin yankin Kudu maso Yamma.

KARANTA KUMA: Wani Mahaifi ya garkame dan sa har na tsawon shekaru 20 a kasar Japan

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, zai gana a yau lahadi da wakilan jam'iyyar na jihohi 19 dake yankin Arewacin Najeriya, yayin da gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha, zai gana da wakilai na jihohin yankin Kudu maso Gabashin kasar domin dabbaka ra'ayin da suka sanya a gaba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel