Nigerian news All categories All tags
Kudin da Buhari zai cire na sayen makamai ya jawo ka-ce-na-ce a Majalisa

Kudin da Buhari zai cire na sayen makamai ya jawo ka-ce-na-ce a Majalisa

- Wani Sanata na Jam’iyyar PDP yace sai da hannun su ne Buhari zai cire kudi

- Shugaba Buhari ya amince da ware Dala biliyan 1 domin yaki da Boko Haram

- Sai dai kuma wasu Sanatocin su na ganin Buhari ba ya bukatar yardar kowa

Mun samu labari daga Jaridar Punch cewa kan Sanatocin Jam’iyyar APC mulki da Sanatocin adawa na PDP ya kara rabuwa a Majalisar Dattawa game da kudin da Shugaba Buhari ya ware na yaki da Boko Haram.

Kudin da Buhari zai cire na sayen makamai ya jawo ka-ce-na-ce a Majalisa

Yakin Boko Haram: An raba hankalin Sanatocin Najeriya

Shugaban kasa Buhari ya amince da ayi amfani da Dala Biliyan 1 na kudin kasar nan wajen sayo makaman da za a yaki ‘Yan ta’addan Boko Haram. Wasu Sanatocin sun ce sai da sa hannun su ne za a cire wannan makudan kudi a kasar.

KU KARANYA: Su wa za su ba Shugaba Buhari ciwon kai a 2019?

Wasu a Majalisar kuma su na ganin cewa ba su da hurumi a dokar kasa tun da Majalisar tattalin arzikin kasar watau NEC tayi na’am da hakan. Mai magana a madadin Majalisar Wakilai Abdulazeez Namdas dai bai ce komai ba tukun har yanzu.

Wani babban Sanatan PDP a kasar Ben Murray-Bruce ya bayyana cewa sai Shugaba Buhari ya nemi amincewar su kafin ya kashe kobo daga cikin wannan makudan kudi. Shi kuma wani babban Sanatan APC Sola Adeyeye ya karyata Ben Bruce.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel