Nigerian news All categories All tags
Hukumar EFCC ta gano yadda jami’an Gwamnati ke satar dukiyar al’umma

Hukumar EFCC ta gano yadda jami’an Gwamnati ke satar dukiyar al’umma

- EFCC tayi wani babban taro da Hukumar BPP mai bada kwangiloli

- Shugaban BPP Mamman Ahmadu ya halarci wannan zama da aka yi

- Magu yace a wajen bada kwangila ake sace kudin Gwamnati a kasar

Mun samu labari daga Jaridun kasar nan cewa Shugaban Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin kasa zagon kasa Ibrahim Magu ya bayyana yadda Ma’aikatan Gwamnati ke satar kudi a Najeriya.

Hukumar EFCC ta gano yadda jami’an Gwamnati ke satar dukiyar al’umma

Shugaban EFCC ya gargadi Ma’aikatan Gwamnati kan aiki da kasafin kudi

Shugaban na Hukumar EFCC ya bayyana cewa Jami’an Gwamnati na satar kudin jama’a ne ta hanyar bada kwangila. Ibrahim Magu ya gargadi Ma’aikatan Gwamnati da su bi kasafin kudin da su ka mikawa Majalisar kasar.

KU KARANTA: Abin da ya sa na bar Majalisar dinkin Duniya na dawo Kaduna

Ibrahim Magu ya nuna cewa duk ma’aikacin da aka samu da badakala a kwangila zai wuce gidan yari don haka sai su yi taka-tsan-tsan. Magu ya rabbatar da cewa babu wanda zai kawo masu cikas wajen yakin da su ka sa gaba.

Shugaban EFCC ya nemi jama’a su tashi tsaye wajen yaki da rashin gaskiya a kasar. Magu ya bayyana wannan ne wajen wani taro da Hukumar BPP mai bada kwangiloli a Najeriya inda Shugaban ta Mamman Ahmadu ya halarta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel