Nigerian news All categories All tags
Sanata Shehu Sani ya caccaki Gwamnonin APC kan rikicin Jam’iyya

Sanata Shehu Sani ya caccaki Gwamnonin APC kan rikicin Jam’iyya

- Jam’iyyar APC tana ta fama da rikicin shugabanci a halin yanzu

- Shugaba Buhari ya nemi John Oyegun ya tattara ya bar kujerar sa

- Sanata Shehu Sani ya caccaki Gwamnonin da su ka sabawa Buhari

Sanatan Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattawa Shehu Sani ya tsoma bakin sa cikin rikicin da ake ta fama da shi a Jam’iyyar APC mai mulki inda wasu ke nema su kara wa’adin Shugaban Jam’iyyar na kasa John Odigie-Oyegun.

Sanata Shehu Sani ya caccaki Gwamnonin APC kan rikicin Jam’iyya

Sanatan da ke wakiltar Garin Kaduna yayi magana kan rikicin APC

Shugaban kasa Muhammadu Buhari dai ya nuna rashin goyon bayan sa ga kara wa’adin John Oyegun. Sai dai wasu Gwamnoni sun yi tirjiya inda su ka nuna cewa bai dace a nemi ayi wani sabon zaben Shugabanni ba a Jam’iyyar.

KU KARANTA:

Sanatan na Kaduna Shehu Sani a shafin sa na Tuwita ya bayyana cewa Gwamnonin da su ka ja da Shugaba Buhari a wannan maganar ba a kira su Makiyan Shugaban ba sai dai ‘Yan Majalisar da su ka nemi a sauya tsarin zabe.

Gwamnonin APC dai sun karyata cewa sun samu sabani da Shugaban kasa Buhari game da rikicin shugabancin Jam’iyyar. Kwanan nan dai Majalisa ta huro wuta cewa sai an maida zaben Shugaban kasa zuwa ranar karshe a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel