Nigerian news All categories All tags
Lalacewa: Nafi jin dadin saduwa da kananan yara - Wani mutum da ya yiwa karamar yarinya fyade

Lalacewa: Nafi jin dadin saduwa da kananan yara - Wani mutum da ya yiwa karamar yarinya fyade

- Wani magidanci mai yara biyar, Tunde Vincent ya shiga hannun Yan sanda bisa tuhumar yiwa karamar yarinya fyade

- Wannan lamarin ya faru ne a kauyen Madalla dake karamar hukumar Suleja a jihar Neja

- Bayan ya amsa laifinsa, ya shaidawa manema labarai cewa baya jin dadin tarawa da manyan mata shiyasa yake neman yara

Hukumar Yan sanda ta damke wani magidanci mai shekaru 25 da laifin yiwa karamar yarinyar 'yar shekara 12 fyade a garin Madalla da ke umar Suleja dake jihar Neja.

Rahotanni sun bayyana cewa magidancin mai yara biyar ya tare yarinyar ne a hanyar ta na zuwa gida, ya kuma jata zuwa wani kango inda yayi mata fyaden.

Nafi sha'awar kananan yara, inji wani katon banza da yayiwa 'yar shekara 12 fyade

Nafi sha'awar kananan yara, inji wani katon banza da yayiwa 'yar shekara 12 fyade

DUBA WANNAN: An kama shi ya daskaras da gawar mahaifiyarsa na tsawon shekaru 3 don yaci gaba da karabar fanshonta

Yayin hirar sa da manema labari a ranar Alhamis, wanda ake zargin yace, "Bani sha'awar saduwa da manyan mata; nafi son tarawa da kananan yara duk lokacin da nake son biyar bukata na; duk lokacin da nayi niyyar denawa sai kuma wani abu ya sake tunzura ni."

Kakakin hukumar Yan sanda na jihar Neja, Muhammad Abubakar, ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya kara da cewa wanda ake zargin ya amsa laifin sa bayan jami'an Yan sanda na Madalla sun kama shi.

Abubakar kuma yace hukumar ta kamalla bincike kuma nan da dan lokaci kadan za'a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu don a yanke masa hukuncin da yayi daidai da laifinsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel