Nigerian news All categories All tags
Yanzu-Yanzu: An kama mutum 7 da ake zargi da hannu cikin fashin Offa

Yanzu-Yanzu: An kama mutum 7 da ake zargi da hannu cikin fashin Offa

A yau Asabar ne Yan sanda a Jihar Kwara suka bayar da sanarwan kama mutane bakwai wanda ake tuhuma da hannu cikin mummar fashin banki da akayi a karamar hukumar Offa da tayi sanadiyyar salwantar rayyuka da 17.

Yan fashin sun kai farmaki a garin ne ranar Alhamis inda sukayi fashi a bankuna guda biyar a titin kasuwar Owode. Rahotanni sunce yan fashin sunyi nasarar shiga dakin ajiyar kudade na bankunan kuma sun sace miliyoyin naira.

Yanzu-Yanzu: An kama mutum 7 da ake zargi da hannu cikin fashin Offa

Yanzu-Yanzu: An kama mutum 7 da ake zargi da hannu cikin fashin Offa

Mutane da dama ciki har da jami'an yan sanda sun rasa rayyukansu, wasu kuma sun samu munanan raunuka sakamakon harin wanda ya bar mutane cikin hawaye da juyayi.

DUBA WANNAN: Sunayen barayin gwamnati: Ko dai a bani hakuri, ko kuma mu hadu a kotu - Dokpesi

Kwamishinan yan sanda na jihar Kwara, Lawan Ado ya shaida wa manema labarai a ranar Asabar cewa mutane 17 ne suka rasu sakamakon fashin. Ya kara da cewa yan fashin sun gudu sun bar wasu motoci wanda yan sanda suka gano.

"A halin yanzu an kama mutane bakwai da ake zargi suna da hannu cikin fashin. An kama mutum daya a Igosun, inda sauran yan fashin suka shige yadda motocin su suka shige daji. An dako motocin an kawo su ofishin yan sanda inda ake cigaba da bincike.

"Mutane 17 ne suka rasa rayyukansu ciki har da yan sanda 9 da kuma farar hula 8. Bankuna guda biyar ne akayi wa fashi a harin," inji Ado.

KU KARANTA: Sunayen barayin gwamnati: Ko dai a bani hakuri, ko kuma mu hadu a kotu - Dokpesi

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel