Nigerian news All categories All tags
Yadda gasar wasanni ta hukumar Sojin Sama ta kaya a jihar Akwa-Ibom

Yadda gasar wasanni ta hukumar Sojin Sama ta kaya a jihar Akwa-Ibom

Da sanadin kakakin hukumar Sojin Sama ta Najeriya, Air Vice Marshal Olatakunbo Adesanya, mun samu rahoton cewa dakarun hukumar sun lashe gasar wasanni na shekarar 2018 da ta saba gudanarwa a tsakanin hukumomi masu damara dake fadin kasar nan.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne wanda tayi daidai da 6 Afrilu, 2018, aka kammala gasar wasanni da aka fara gudanarwa tun a ranar 3 ga watan Afrilu kamar yadda ta saba a kowace shekara cikin shekaru uku da suka gabata.

Rahotanni sun bayyana cewa, an gudanar da gasar ne a farfajiyar wasanni ta Godwill Akpabio International Stadium dake birnin Uyo na jihar Akwa Ibom, inda rundunar sojin sama ta GTC ta yi fice cikin rundunoni 6 na hukumar sojin wajen lashe sarkoki 6 na zinare da kuma ta azurfa guda daya.

Legit.ng ta fahimci cewa, hukumar Sojin ta dauki salo na gudanar da wannan wasanni domin karin karsashi ga dakarun ta, inda gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel ya jagoranci bayar da kyaututtuka ga macancanta na wannan shekara.

KARANTA KUMA: 'Yan sanda sun tsinto gawawwaki 10 a yankunan jihar Benuwe

Gwamnan ya kuma bayar da kyautar zunzurutun kudi har na N2m ga dakarun da suka samu nasarar a wannan shekara tare da yabawa shugaban hafsin sojin saman Air Vice Marshal Sadique Abubakar, dangane da wannan sabon salo da ya kawo na karawa dakarun karsashi da zai taimaka wajen sauke nauyin da rataya a wuyan su.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, akwai wasu jerin nau'ikan abinci goma dake kawar da wari da kuma gafin jiki gami da kamsasa shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel