Nigerian news All categories All tags
Rudani: Ana rade-raden yaduwar kifin roba a kasuwannin Najeriya

Rudani: Ana rade-raden yaduwar kifin roba a kasuwannin Najeriya

Hukumar nan ta gwamnatin tarayya da ke da alhakin kula da lafiyar abinci da magunguna a Najeriya watau National Agency for Food and Drug Administration and Control (NAFDAC) ta tabbatar da cewa babu wani kifin roba dake yawo a kasuwannin Najeriya.

Wannan sanarwar dai kamar yadda muka samu ya ta fito ne daga bakin mahukuntan hukumar a yayin wata fira da manema labarai da suka yi a ranar Alhamis din da ta gabata.

Rudani: Ana rade-raden yaduwar kifin roba a kasuwannin Najeriya

Rudani: Ana rade-raden yaduwar kifin roba a kasuwannin Najeriya

KU KARANTA: Iyalan Gwamna Yahaya Bello sun tsallake rijiya da baya

Legit.ng dai ta samu cewa a baya wani dan Najeriya ne yayi korafin cewa ya sayi wani irin kifin da yaki dahuwa duk kuwa da irin wutar da yayi ta gwalala masa na tsawon lokaci inda yayi zargin kifin na roba ne.

A wani labarin kuma, Kusan kimanin kwanaki kadan da turgudewar Gwamnan jihar Kogi Gwamna Yahaya Bello yayin da yake kokarin sauka daga mota, a jiya kuma shugaban ma'aikatan sa, mata da kuma dan sa suma wani hatsarin ya rutsa da su.

Mun samu dai cewa hatsarin ya rutsa da iyalan na sa ne a kan hanyar su ta Abuja zuwa Lokoja inda aka ruwaito cewa motar ta kwace ma diriban ne amma kuma cikin ikon Allah ba wanda ya rasa ran sa amma yanzu haka suna asibi domin samun kulawa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel