Nigerian news All categories All tags
An yankewa wani Kare hukuncin kisa da laifin kashe Ubangidan sa

An yankewa wani Kare hukuncin kisa da laifin kashe Ubangidan sa

Rahotanni da sanadin shafin jaridar The Punch sun bayyana cewa, an zartar da hukuncin kisa kan wani Kare a ranar Juma'ar da ta gabata bayan da bincike ya tabbatar da cewa shi yayi sanadiyar mutuwar Ubanidan sa a birnin Hanover dake kasar Jamus.

Wannan lamari ya janyo cecekuce a kasar ta Jamus yayin da muhawarori da musayar ra'ayi suka barke a tsakanin al'ummar ta dangane da dokokin da suke tattare da mallakar Kare.

Bincike ya tabbatar da cewa, wata tsohuwar mata mai shekaru 52 da kuma dan ta mai shekaru 27 sun riga mu gidan gaskiya a sakamakon farmaki da Karen ya kai musu a gidan su.

An yankewa wani Kare hukuncin kisa da laifin kashe Ubangidan sa

An yankewa wani Kare hukuncin kisa da laifin kashe Ubangidan sa

Hukumomin tsaro sun cafke wannan Kare bayan da suka balle kofar gidan tsohuwar matar a yayin da 'yar ta ta nemi ganawa da su ta hanyar wayar sadarwa amma babu wanda ya dauki kiranta tun a ranar Talatar da ta gabata.

KARANTA KUMA: Hukumar Sojin Kasa ta cafke Barayin Shanu 4 a jihar Bauchi

Makwabta dai sun bayyana cewa, marigayi dan wannan tsohuwar mata ya sha fama da jinya tun yana dan kankani gami da ita kuma tsohuwar mai amfani da kujerar guragu sakamakon shekarun da suka ja.

A halin yanzu dai wannan Kare mai sunan Chico yana nan a wurin ajiyar dabbobi dake garin Langenhagen kafin a dabbaka hukuncin da aka zartar a gare shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel