Nigerian news All categories All tags
An bukaci fadar shugaban kasa da sauran ma'aikata su bayyana kudaden suke kashewa wajen hidimar ofisoshinsu

An bukaci fadar shugaban kasa da sauran ma'aikata su bayyana kudaden suke kashewa wajen hidimar ofisoshinsu

- Har yanzu ana cigaba da tafka mahawara a kan adadin kudaden da yan majalisar tarayya ke ware wa don gudanar da ayyukansu

- Kungiyar masu taimakawa ma'aikatan majalisar tarayya (CONASSLA) sun tsoma baki cikin mahawarar

- Kungiyar ta kallubalanci sashin gudanarwa na gwamnati suma su bayyana adadin kudaden da suke kashewa wajen tafiyar da ayyukansu

Kungiyar masu taimakawa ma'aikatan majalisar tarayya (CONASSLA) sun bukaci gwamnatin tarayya ta bayyanawa al'ummar Najeriya adadin kudaden da shugaban kasa da matarsa da gwamnoni da ministoci ke karba a kowane wata don tafiyar da ayyukansu don tabbatar da gaskiyarsu. Kungiyar ta kunshi tsofaffi da sabbin ma’aikatan majalisun.

Kungiyar mataimakan 'Yan majalisa sun kallubalanci sauran ma'aikatun gwamnati su bayyana albashin su

Kungiyar mataimakan 'Yan majalisa sun kallubalanci sauran ma'aikatun gwamnati su bayyana albashin su

Legit.ng ta ruwaito cewa ma’aikatan sun fadi bukatarsu a wani jawabi da suka aika masu a ranar Juma’a 6 ga watana Afirilun 2018, wanda Abdullahi Mustapha ciyaman na kungiyar da Funmi Oyekan sakataren kungiyar suka sanya hannu.

KU KARANTA: Muhimman abubuwa 6 da Iyabo Obasanjo ta fadi ma babanta a sabuwar wasikarta gareshi

Kungiyar tace “Wannan bukatar ya taso ne sakamakon yadda Majalisar Tarayya suka bayyana kudaden tafiyar da ayyukan sanatoci a kasafin kudi na 2018, abinda aka samu shugaban kasa kadai ya ware wa kansa kudi N900m don kula da motocinsa a 2018; Mai bawa shugaban kasa shawara ta fannini tsaro ya rubuto nasa kasafin na N1.14bn na shara da goge ofishinsa a 2018; sai ministan sufuri yana bukatar N10bn don mototcin tafiye tafiyensa a 2018.

“Banda hukumar tsaro ta jiha da take shirin kashe sama da N2.2bn akan kafar sadarwa, sai ministan sadarwa ya shirya karbar $800,000, idan ka hada wannan kudaden nawa zaka samu, shi yasa muka bukaci su bayyana wa mutane idan suna da gaskiya”.

Hakan ne yasa kungiyar ta kallubalanci sashin ayyuka na gwamnatin tarayya ta bayyanawa al'umma adadin kudaden da take kashewa wajen tafiyar da harkokin ofisoshinsu da kuma adadin da kowa yake karba cikin kwanakin bakwai.

A wata labarin kuma, wata kungiya mai zaman kanta ta shawarci gwamnatin tarayya ta karkatar da akallar yaki da rashawa akan ma'aikatu da hukumomin ba wai yan siyaa ba kawai don magance rashawar baki daya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel