Abin takaici: Kwandasta yayi lalata da 'yar 11, har ta fara yoyon fitsari

Abin takaici: Kwandasta yayi lalata da 'yar 11, har ta fara yoyon fitsari

- Ana kara samun laiffuka na lalata da kananan yara a sassan Najeriya

- Wannan wani kwandasta ne da ya lalata yar 11 har ta kasa ajje fitsari

- Daga wasan mata-da miji ashe wayo yake yi mata

Abin takaici: Kwandasta yayi lalata da 'yar 11, har ta fara yoyon fitsari

Abin takaici: Kwandasta yayi lalata da 'yar 11, har ta fara yoyon fitsari

Daga wasan mata-ta zo in baki alawa, shegen ashe lalata musu 'ya zayyi; Kwandasta dan shekara 40 ya haike wa wata karamar yarinya 'yar shekara goma da daya da lalata, a lokuta da dama, har ta kai yanzu bata iya rike fitsari.

Baba Michae, mazaunin Legas, wanda aka kama a talatar nan, ya amsa laifinsa, kuma ga alama har abun ya kai ga rahoton likita. Ance dai shi mutum ne mai kunya kuma kar na kirki, wanda hakan ya sanya abin ya baiwa kowa mamaki.

Sai dai ba abin mamaki bane, domin dama sha'awa tafi damun masu kunya wadanda basu iya tsara mace ko neman wadda tayi wayo.

DUBA WANNAN: Kisan gilla a Offa: Yadda ta kasance a jiya

An dai kula da matsalar ne, bayan da ta kasa ajje fitsari yayin da ake jarrabawa, lokuta da dama a rana daya, lamari da ya sanya aka gaya wa iyayenta, su kuma suka kaita asibiti, likita kuwa ya gano me yake faruwa.

Kaico!

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel