Nigerian news All categories All tags
Majalisa tayi tir da kudade da aka ware har tiriliyan daya da rabi don yaye talauci

Majalisa tayi tir da kudade da aka ware har tiriliyan daya da rabi don yaye talauci

- Sanatoci sunyi watsi da tabbatar da N1.5 tiriliyan da aka ware domin shirin hannun jari

- A jiya ne sanatoci suka kalubalanci tabbatar da Naira tiriliyan daya da rabi domin zuba su a shirin walwala, sun kwatanta shi da barna

- Sanatocin sun nuna rashin amfanin hakan ne domin kuwa yan'najeriya bazasu ga amfanin shirin ba

Majalisa tayi tir da kudade da aka ware har tiriliyan daya da rabi don yaye talauci

Majalisa tayi tir da kudade da aka ware har tiriliyan daya da rabi don yaye talauci

Sunyi alhinin cewa cewa a hankali shirin zai bi hanyar da shirin karin hannun jari na tallafin man fetur da karfafa (SURE-P) wanda Gwamnatin Goodluck Jonathan ya fito da shi. Kuma sun tsoratar da cewa kudin da za a ware ma shirin Naira biliyan dari biyar zai zama asara.

Shugaban kwamitin akan cancanta, sanata Mohammed Danjuma Goje, ya tsoratar a yayin da mai ba shugaban kasa shawara ta musamman a kan hannun jarin walwala Mrs Maryam Uwais ta bayyana a gaban kwamitin.

DUBA WANNAN: Zamfara ce ta-kashin baya a harkar Boko a duniya

Mai bada shawarar ta sanar da kwamitin cewa ofishin zuba hannu jari a kan walwala (NSIO) ya karba N175 biliyan a shekarar 2016 da kuma 2017,ba biliyan 500 ba.

Mrs Uwais tace "zaku iya tunawa da cewa biliyan 500 aka warewa NSIO a 2017,wanda a cikinta aka ware biliyan 100 domin gina gidaje a karkashin bangaren kudi na tarayya.

Sannan a cikin ragowar biliyan 400, biliyan 90 aka ba ma NSIO na shekara 2017" ta kara da cewa sun karba biliyan 85 a 2016.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel