Nigerian news All categories All tags
Matasan kudu maso arewa sunyi jinjina ga Buhari akan cigaban da ya kawo

Matasan kudu maso arewa sunyi jinjina ga Buhari akan cigaban da ya kawo

- Kungiyar matasan Kudu Maso Arewacin Najeriya (SWYM) wanda ya hada da jihohi shida na yankin sunjyi jinjina ga Muhammadu Buhari bisa ga cigaban da ya kawo

- Ciyaman na SWYM Temitope Ogunlade ya bayyana jinjinar a taron labarai a birnin tarayya

- Ogunlade yace kungiyar ta duba shirin da gwamnatin Buhari keyi tun hawanta mulki a shekarar 2015 kuma sun gane cewa ana karuwa

Kungiyar matasan Kudu Maso Arewacin Najeriya (SWYM) wanda ya hada da jihohi shida na yankin sunjyi jinjina ga Muhammadu Buhari bisa ga cigaban da ya kawo. Ciyaman na SWYM Temitope Ogunlade ya bayyana jinjinar a taron labarai a birnin tarayya.

Ogunlade yace kungiyar ta duba shirin da gwamnatin Buhari keyi tun hawanta mulki a shekarar 2015 kuma sun gane cewa ana karuwa.

Ogunlade ya kara da cewa ma’aikatar wutar lantarki da ayyuka da gidaje a karkashin gwamnatin shugaba Buhari ta saki kasafin kudi wanda ya sake tayar da tsofaffin gine-gine.

Yace a karkashin mulkin Buhari aka kirkiro da shirin Social Safety Net, wanda shiri ne da ba’a taba samun shiri kamarsa ba a tarihin Najeriya sannan sai shirin N-Power wanda ya samarwa matasa da dama aikinyi wanda ake biyansu N30,000 duk wata.

KU KARANTA KUMA: Fadar shugaban kasa ta kare Buhari akan amincewa da bayar da $1bn na tsaro

Bayan haka gwamnatin ta kawo shiri na bayarda abinci ga yara ‘yan makarantar primary abinci a makarantu sama da 8,587 ajihohi 19, bugu da kari ta dauki mutane wadanda zasu ringa dafa abincin. Ga kamfanin mai da ta gina a yankin Niger Delta don magance rashin aikinyi da rashin mai a yankin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel