Nigerian news All categories All tags
Sakataren gwamnatin tarayya ya bukaci hukumar EFCC da ta kula da cin hanci a ma’aikatu

Sakataren gwamnatin tarayya ya bukaci hukumar EFCC da ta kula da cin hanci a ma’aikatu

- Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya bukaci hukumar dake kula da yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa data kula da cin hanci a ma’aikatu

- Daraktan labarai na Ofishin sakataren gwamnatin tarayya Lawrence Ojabo, yace sakataren gwamnatin tarayyar yayi kiran ne lokacin da shugaban hukumar kula da tattalin arzikin kasa Ibrahim Magu ya kai masa ziyara a Ofishinsa

- Mustapha ya bukaci hukumar da tayi amfani da hanyar wayarwa mutane da kai game da illolin cin hanci game da aikin gwamnati

Sakataren gwamnatin tarayya Boss Gida Mustapha yayi kira ga hukumar dake kula da yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa databulo da wata hanya da zatayi amfani da ita ta magance cin hanci a kowane mataki na gwamnati.

Mustapha ya shawarci shugaban hukumar kula da tattalin arzikin kasa Ibrahim Magu tareda mutanensa lokacin da suka kai masa ziyara a Ofishinsa a ranar Juma’a, a birnin tarayya.

Sakataren gwamnatin tarayya ya bukaci hukumar EFCC da ta kula da cin hanci a ma’aikatu

Sakataren gwamnatin tarayya ya bukaci hukumar EFCC da ta kula da cin hanci a ma’aikatu

Daraktan labarai na Ofishin sakataren gwamnatin tarayya Lawrence Ojabo, yace sakataren gwamnatin tarayyar ya bukaci hukumar da tayi amfani da hanyar wayarwa mutane da kai game da illolin cin hanci game da aikin gwamnati ya kuma tabbatar masu da zaman lafiya aje aiki.

KU KARANTA KUMA: Fadar shugaban kasa ta kare Buhari akan amincewa da bayar da $1bn na tsaro

Bayan sakataren yayi jinjina ga jami’an sannan ya kara da cewa komawarsu sabon Ofishinsu da ake ginawa a birnin tarayyar zai taimaka masu wurin gudanar da ayyukansu a bincike yanda ya kamata, duk da hasarinsa.

Magu bayan ya masa bayani akan matsayin da aikin ginin yake na gab da karashe, ya bukaci sakataren gwamnatin da ya kai ziyara a sabuwar Helikwatar tasu wadda ake ginawa a birnin tarayyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel