Nigerian news All categories All tags
Hukumar NEMA ta dakatar da manyan daraktoci 6

Hukumar NEMA ta dakatar da manyan daraktoci 6

Hukumar dake bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta dakatar da daraktocinta guda shida har ila masha Allah bisa bincike da take gudanarwa kan ayyukan cin hanci da rashawa a hukumar.

Sani Datti, kakakin hukumar ta NEMA a wata sanarwa da aka fitar a ranar Juma’a ya bayyana cewa sabon kwamitin da hukumar ta nada sakamakon biniken kudin NEMA da hukumar EFCC keyi ne ta dakayar da daraktocin.

Ya kara da cewa kudaden shekarun da hukumar yakin da cin hanci ke bincike sun fara ne daga shekarar 2011 zuwa 2015.

A cewarsa, wadanda aka dakatar sun hada da daraktan kudi da asusu, Akinbola Hakee Gbolahan; Darakta mai rukon kwarya na ayyuka na musamman, Mista Umesi Emenike; Daraktan kula da rage hatsari, Mallam Alhassan Nuhu, Matukin jirgi dake kula da jiragen agajin gaggawa, Mista Mamman Ali Ibrahim, shugaban kula harkokin hukumar, Mista Ganiyu Yunusa Deji da kuma daraktan kula da jin dadin jama’a, Mista Kanar Mohammed.

KU KARANTA KUMA: Fadar shugaban kasa ta kare Buhari akan amincewa da bayar da $1bn na tsaro

Datti yace hukumar EFCC a wani rahoto da ta aika ga fadar shugaban kasa ta bayar da shawarar daukar mataki domin samar da damar bincike da kuma samun muhimman rahotanni kan zargin rashawa da ake yiwa daraktocin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel