Nigerian news All categories All tags
Fadar shugaban kasa ta kare Buhari akan amincewa da bayar da $1bn na tsaro

Fadar shugaban kasa ta kare Buhari akan amincewa da bayar da $1bn na tsaro

- Mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina yace wadanda ke adawa da amincewar shugaba Buhari akan bayarda $1bn na tsaro suna yin siyasa ne da rayukan ‘yan Najeriya

- Ministan tsaro Brig-Gen. Mansur Dan-Ali, ya bayyana cewa shugaba Buhari ya bayar da umurnin sakin kudi $1bn don siyo makaman da suka kamata don magance rashin tsaro

- Kungiyar zartarwa ta tattalin arzikin kasa a shekarar 2017, sun amince da $1bn, wanda za’a samu ta fannin kudin danyen mai don magance rashin tsaro da ta’addanci a fadin kasar

Mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina yace wadanda ke adawa da amincewar shugaba Buhari akan bayarda $1bn na tsaro suna nuna siyasa ne da rayukan ‘yan Najeriya.

Ministan tsaro Brig-Gen. Mansur Dan-Ali, lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan taron tsaro tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana shugaban kasar ya bayar da umurnin sakin kudi $1bn don siyo makaman da suka kamata don magance rashin tsaro.

Kungiyar zartarwa ta tattalin arzikin kasa (NEC) a shekarar 2017, sun amince da $1bn, wanda za’a samu ta fannin kudin danyen mai don magance rashin tsaro da ta’addanci a fadin kasar.

Fadar shugaban kasa ta kare Buhari akan amincewa da bayar da $1bn na tsaro

Fadar shugaban kasa ta kare Buhari akan amincewa da bayar da $1bn na tsaro

Sakataren jam’iyyar PDP Kola Ologbondiyan a ranar Alhamis,a birnin tarayya, ya bayyana rashin amincewarsu da wannan kudiri na shugaba Buhari akan bayarda $1bn don magance rashin tsaro a kasar, ba tare da wani jawabi daga majalissar zartarwa ba.

KU KARANTA KUMA: Rayuwa a matsayinka na dalibi a makarantar Boko Haram

Adesina ya mayarwa PDP da murtani a ranar Alhamis da daddare lokacin da yake zantawa da gidan Talabijin na Channels, inda yace anbi ka’idojin da suka kamata wurin sakin wadannan kudade. Yace shugaban kasar zai yiwa majalissar bayani ta hanyar babban mataimakinsa na harkokin majalisar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel