Nigerian news All categories All tags
Matasan arewa sunyi gargadi mai tsanani ga Obasanjo kan sukar gwamnatin Buhari

Matasan arewa sunyi gargadi mai tsanani ga Obasanjo kan sukar gwamnatin Buhari

- Kungiyar matasan arewa ta cacaki tsohon shugaba Olusegun Obasanjo kan yadda yake sukar shugaba Buhari

- Kungiyar ta shawarci Obasanjo ya kyale 'yan Najeriya su zabi wanda suke so a zaben na 2018

- Kungiyar ta kuma duk da cewa akwai wasu kurakurai da Buhari yayi, gwamma shi a kan Obasanjo

Kungiyar matasan arewa a turence 'Arewa Consultattive Forum' (ACF) ta ja kunnen tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, daya daina fadawa 'yan Najeriya da kada su sake zaben shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019 mai zuwa.

Matasan arewa sun yi gargadi mai tsanani ga Obasanjo kan sukar gwamnatin Buhari

Matasan arewa sun yi gargadi mai tsanani ga Obasanjo kan sukar gwamnatin Buhari

KU KARANTA: Sakataren gwamnatin tarayya ya bayar da shawara kan yadda za'a magance rashawa a ma'aikatun gwamnati

Gargadin na kunshe ne ciki bayanin da shugaban kungiyar, Alhaji Yerima Shettima ya sawa hannu yau juma'a. Bayanin gargadin na cewa: "Lokuta da yawa, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo na nuna kamar shi wanda zai ceton yan Najeriya ne, ta haska yadda shugabanci da siyasar kasar nan zai kasance. Wannan halayya tashi ba abinda take haifarwa kasar nan sai masifa."

Kungiyar ta bayyana cewa katsalandan din da tsohon shugaban kasar nan ke yi a sha'anin mulkin kasar nan abin kaico ne duba da kassara kasar nan da ya yi a zamanin mulkinsa.

"Ba za mu ce shugaban kasa na yanzu ba shi da kusakurai ba, amma babu shaka ya fi Obasanjo sau dubu. Kuma muna kalubalantar Obasanjo ya gaya mana dalilin daya haifar mana da matsin tattalin arziki da babu sa hannun da shisshiginsa a ciki.

"Don haka, babu wani tsoho kwaya daya tak da zai zauna ya yankewa mutane milyan dari da sittin 160,000,000 hukuncin abinda kasar su za ta zama."

Jawabin nasu ya karkare da cewa: "Wannan gargadi muke yi, in kunne ya ji, gangan jiki ya tsira"

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel