Nigerian news All categories All tags
Akwai dimbin ayyukan gwamnati shugaba Buhari da ba'a bayyanawa - Oyo-ita

Akwai dimbin ayyukan gwamnati shugaba Buhari da ba'a bayyanawa - Oyo-ita

- Shugaban ma'aikata na kasa Winifred Oyo-Ita tace gwamnatin Muhammadu Buhari ta samu cigaba da dama a watannin da suka gabata

- Tace kafafen yadda labarai suna rage abubuwa da dama a cikin abubuwan cigaba da Buhari ya kawo a kasar nan

- Oya-Ita ta bukaci a karawa ma’aikatar labarai da al’adu kudade don gudanar da ayyukansu yanda ya kamata

Akwai dimbin ayyukan shugaba Buhari da ba'a bayyanawa - Oyo-ita

Akwai dimbin ayyukan shugaba Buhari da ba'a bayyanawa - Oyo-ita

Shugaban ma'aikata na kasa Winifred Oyo-Ita tace gwamnatin Muhammadu Buhari ta samu cigaba da dama a shekaru biyu da suka gabata suka gabata, wadanda ba’a bayyanawa mutane ba.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun gano bindigogi 107 a jihar Anambra

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Oyo-Ita ta bayyana cewa kafafen yadda labarai suna rage abubuwa da dama cikin abubuwan cigaba da Buhari ya kawo a kasar nan, a ranar Alhamis 5 ga watan Afirilu a birnin tarayya, lokacinda suka kai ziyara ga sakatarorinma’aikatar labarai da al’adu.

Legit.ng ta ruwaito cewa a karkashin shugaban ma'aikatan sun kirkira Sakatarorin bangarorin ma’aikatar ne don inganta ayyukan bangarorin maikatar na (MDAs). Oya-Ita ta bukaci a karawa ma’aikatar labarai da al’adu kudade don gudanar da ayyukansu yanda ya kamata

Oya-Ita ta gargadi gidajen Talabijin masu nuna finafinan yara da cewa suyi taka tsan-tsan, saboda akwai wadanda ke koyawa yara madugo da luwadi. Ta kumayi jinjina ga Satariyar ma’aikatar Grace Gekpe akan kokarin da tayi wurin samun 94% na kasafin ma’aikatar a shekarar 2017.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel