Nigerian news All categories All tags
Yadda gwamnati ta gyara jirgin $2.8m akan $18m kusan ninkin farashinsa sau bakwai

Yadda gwamnati ta gyara jirgin $2.8m akan $18m kusan ninkin farashinsa sau bakwai

- Mbu tsohon Minista ne da ya jagoranci tsaronn kasar nan

- A littafinn nasa ya rubuta yadda a zamanin Muhammadu Ribadu aka sayo jirgin

- Ya rasu a 2012, amma a makon gobe ne za'a kaddamar da littafin nasa

Yadda gwamnati ta gyara jirgin $2.8m akan $18m kusan ninkin farashinsa sau bakwai

Yadda gwamnati ta gyara jirgin $2.8m akan $18m kusan ninkin farashinsa sau bakwai

A sabon littafi da Mista Matthew Mbu ya rubuta kafin rasuwarsa a 2012, ya zayyana yadda aka tafka cuwa-cuwa a lokacin yana gwamnati, a ma'aikatar tsaro wadda yayi wa Minista.

A littafin, ya ayyana yadda ya cancana kudin Najeriya, amma bayan tafiyarsa, sai kawai aka cinye kudin aka kuma taka almundahana, inda jirgin yakin na ruwa da ya sayo a dala miliyan kusan uku, aka ce za'a yi masa kwaskwarima a dala miliyan 18.

A littafin dai, mai taken 'Rayuwar sadaukar da kai' Littain Matthew Mbu, an zayyano yadda aka kwana a ragaya da ma yadda aka kashe makudan kudade a jiharsa ta Cross Ribas, a Tinapa, inda yace nan ma almubazzaranci ne.

DUBA WANNAN: Tallafin man fetur ya kai Tiriliyan 1.4 a kasar nan - Kachikwu

A karshe, littafin zai sami zayyana a Abuja, ta hannun dansa Matthew Mbu Jr. inda za'a kaddamar da shi 10 ga watan nan na Afrilu a Abuja a Yar'aduwa Centre dake tsakiyar gari.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel