Nigerian news All categories All tags
Tallafin Man Fetur ya kai tiriliyan 1 da biliyan 400 na nairori, Kachiku ya bayyana

Tallafin Man Fetur ya kai tiriliyan 1 da biliyan 400 na nairori, Kachiku ya bayyana

- Gwamnatin tarayya tace tsarinta na shekara akan tallafin man fetur ya daga zuwa sama da N1.4 trillion. Karamin ministan man fetur, ya bada sabon adadin a ranar alhamis a Abuja

- Adadin ya nuna cewa kimanin biliyan N23.99 gwamnati ke kashewa duk wata domin tallafin man fetur

- Tallafin man fetur ya daga da kashi 81 cikin dari zuwa N1.4 trillion- Kachikwu

Tallafin Man Fetur ya kai tiriliyan 1 da biliyan 400 na nairori, Kachiku ya bayyana

Tallafin Man Fetur ya kai tiriliyan 1 da biliyan 400 na nairori, Kachiku ya bayyana

Tallafin man fetur ya daga da kashi 81 cikin dari zuwa N1.4 trillion-kachikwu. Gwamnatin tarayya tace tsarinta na shekara akan tallafin man fetur ya daga zuwa sama da N1.4 trillion. Karamin ministan man fetur, ya bada sabon adadin a ranar alhamis a Abuja.

Sabon adadin yayi kusan kashi 81 bisa dari na tsohon adadin naira miliyan 774 wanda shugaban matatar man fetur na kasa, Maikanti Baru ya bada a biyar ga watan Maris, 2018 domin shigowa da kuma rarraba man fetur a kasar.

Adadin ya nuna cewa kimanin biliyan N23.99 gwamnati ke kashewa duk wata domin tallafin man fetur.

Mista Kachikwu yayi maganar ne a wani taron gogarwa wanda sashen da ke kulada albarkatun man fetur na Gwamnatin tarayya ta shirya a Abuja.

Yace tashin adadin ya samo asali ne da cewa matatar man fetur ta kasa ita ce kadai ke madogara ta shigowa da kuma rarraba man fetur ta kasar.

DUBA WANNAN: Mutum 28 ne suka zana jarrabawar shiga sakandare a Zamfara

Ministan ya kara dangatawa da yanda wasu kananan hukumomi da ke da makwaftaka da kasashen kusa suka dinga safarar man ba ta halastacciyar hanya ba.

Matatar tayi ittifakin kusan jihohi goma sha shida cikin talatin da shida ne suke da makwaftaka da wasu kasashen. Kusan kananan hukumomi 61 suke da gidajen shan mai 2201 wanda suke aiki a cikin jihohin.

Kachikwu yace wannan kalubale dai tuni Gwamnatin tarayya ta kawo karshen shi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel