Nigerian news All categories All tags
Ubangiji ne ya turowa Najeriya Shugaban kasa Buhari – Lai Mohammed

Ubangiji ne ya turowa Najeriya Shugaban kasa Buhari – Lai Mohammed

- Gwamnatin Shugaba Buhari ta zo ne ta ceci jama'a inji Lai Mohammed

- Ministan kasar yace wannan ne lokacin da ya dace da Buhari yayi mulki

- Lai yace Shugaba Buhari ya cika manyan alkawuran da ya dauka a 2015

Ministan yada labarai da al’adu na Najeriya Alhaji Lai Mohammed yace wannan Gwamnatin ta Shugaban kasa Muhammadu Buhari tamkar Ubangiji ne ya kawo ta domin ta cece al’ummar kasar daga barnar Gwamnatin PDP tayi baya.

Ubangiji ne ya turowa Najeriya Shugaban kasa Buhari – Lai Mohammed

Lai Mohammed yace Shugaban kasa Buhari ya cika alkawuran da yayi

Lai Mohammed yace su na alfahari da aikin da su kayi a cikin kasa da shekaru 3 da kafa Gwamnati duk da irin surutun da ‘Yan adawa ke yi a kasar. Mohammed yace Shugaba Buhari ya cika manyan alkawuran da ya daukarwa ‘Yan Najeriya.

KU KARANTA: Mu na tare da Buhari ba za mu biyewa Dattawan Kasar nan ba – Matasan APC

Dama dai abubuwan da Shugaba Buhari yayi alkawari a kan su su ne: Kawo karshen rikicin Boko Haram da yaki da rashin gaskiya da kuma farfado da tattalin arziki. Lai Mohammed yace an cika wannan alkawura daga 2015 zuwa yanzu.

Ministan ya bayyana wannan ne lokacin da wasu manyan ma’aikatan Gwamnatin Tarayyya su ka kai masa ziyara. Mohammed ya kuma bayyana yadda jama’a su ka amfana da tsararen da Gwamnatin Buhari ta kawo na marasa galihu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel