Nigerian news All categories All tags
Hukumar Sojin kasa ta yiwa Dakaru 3,729 karin matsayi na musamman

Hukumar Sojin kasa ta yiwa Dakaru 3,729 karin matsayi na musamman

Da sanadin kakakin hukumar sojin kasa Birgediya Janar Texas Chukwu, mun samu rahoton cewa, shugaban hafsin sojin kasa Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai, ya bayar da lamuni na karin matsayi na musamman ga wasu dakaru 3, 729.

Shugaban hafsin sojin kasa a yayin kara matsayin dakaru

Shugaban hafsin sojin kasa a yayin kara matsayin dakaru

Hukumar ta yiwa wannan adadi na dakaru goma ta arziki dake karkashin rundunar Lafiya Dole a sakamakon jarumtar da suka nuna wajen atisaye mai taken Deep Punch II da suka gudanar a dajin Sambisa.

KARANTA KUMA: An rufe fiye da Masallatai da Coci 6000 a kasar Rwanda sakamakon rashin hali na kula da su

Kakakin hukumar ya bayyana wannan rahoto ne a wata sanarwa ta ranar Alhamis din da ta gabata.

Legit.ng ta fahimci cewa, manufar wannan atisaye na Lafiya Dole da dakarun ke gudanarwa ita ce kawo karshen ta'addancin Boko Haram a yankin Arewa Maso Gabashin kasar nan.

Jaridar ta kuma ruwaito cewa, hukumar Sojin ta sake cafke wasu barayin shanu 4 a jihar Bauchi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel