Nigerian news All categories All tags
Yakin neman kujerar shugabancin APC ya karu sakamakon tsoffin gwamnoni da wasu da suka nuna kwadayinsu a kai

Yakin neman kujerar shugabancin APC ya karu sakamakon tsoffin gwamnoni da wasu da suka nuna kwadayinsu a kai

- A kokarin da akeyi na nada sabon ciyaman na jam’iyyar APC, rudanin ya karu sakamakon shawarar da shuwagabannin kungiyar sukayi na sake zaben jagororin jam’iyyar

- Yanzu rikicin neman kujerar ya karu saboda tsofaffin gwamnoni da sanatoci ne ke neman kujerar ciyaman na jam’iyyar ta APC

- Har yanzu gwamnoni ‘yan jam’iyyar basu bayyana wanda zasu marawa baya ba, amma hankalinsu yafi rinjaye akan wanda zai jagoranci bude kamfen da wadanda za’asa a kwamitin

A kokarin da akeyi na nada sabon ciyaman na jam’iyyar APC, rudanin ya karu sakamakon shawarar da shuwagabannin kungiyar sukayi na sake zaben jagororin jam’iyyar.

Yanzu rikicin neman kujerar ciyaman na jam’iyyar APC ya karu saboda tsofaffin gwamnoni da sanatoci ne ke neman kujerar ta Cif Odigie-Oyegun, wadanda suka hada da tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomole; tsohon shugaban majalisa, Cif Ken Nnamani; da Ministan kimiyya da Fasaha, Dr. Ogbonna Onu.

Yakin neman kujerar shugabancin APC ya karu sakamakon tsoffin gwamnoni da wasu da suka nuna kwadayinsu a kai

Yakin neman kujerar shugabancin APC ya karu sakamakon tsoffin gwamnoni da wasu da suka nuna kwadayinsu a kai

Bincike ya kara nuna cewa tsohon gwamnan jihar Cross River, Chief Clement Ebri, ya bayyana nasa kudurin na shiga cikin masu neman kujerar, Ebri wanda an zabeshi lokacin yana da shekaru 39 a duniya yanata magana da shuwagabannin jam’iyyar akan nasa kudirin.

Har yanzu gwamnoni ‘yan jam’iyyar basu bayyana wanda zasu marawa bay aba, amma hankalinsu yafi rinjaye akan wanda zai jagoranci bude kamfen da wadanda za’asa a kwamitin.

KU KARANTA KUMA: Mun kara kudin Jirgin kasa ne saboda masu kudi sunfi talakawa amfani dashi - Amaechi

Sakataren jam’iyyar ya bayyanawa jami’in manema labaru cewa taron jam’iyyar da zasu gudanar a ranar Litinin yana nan bayan sun karbi rahoto daga kwamitin da gwamna Simon Lalong ke jagoranta, duk da jita-jitar da mutane keyi fada na cewa za’a daga taron.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel