Nigerian news All categories All tags
Tsohon shugaban kasa ya gurgfana gaban Kotu don amsa tuhume tuhumen cin hanci da rashawa

Tsohon shugaban kasa ya gurgfana gaban Kotu don amsa tuhume tuhumen cin hanci da rashawa

Da safiyar ranar juma’a, 6 ga watan Afrilu ne tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu, Jacob Zuma ya bayyana gaban wata Kotu dake mahaifarsa, Kwazulu Natal, bisa badakalar kudin makamai da ake zargin ya wakana a karkashinsa.

Ana tuhumar Zuma ne kan laifuka 16 da suka danganci almundahana, sata da kuma karkatar da wasu makudan kudade, dala biliyan 2.5 da aka ware don siyan makamai a zamanin mulkinsa, kamar yadda kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito.

KU KARANTA: Yan bindiga sun gindaya ma gwamnati sharadin ajiye makamai da zaman lafiya a Zamfara

Sai dai majiyar Legit.ng ta ruwaito Zuman ya musanta dukkanin tuhume tuhumen da ake yi masa, haka kuma ya kalubalanci gwamnatin kasar Afirka ta kudu da cewa bata da hurumin shigar da shi kara.

Tsohon shugaban kasa ya gurgfana gaban Kotu don amsa tuhume tuhumen cin hanci da rashawa

Zuma a Kotu

Wannan shari’a ta Zuma ta zama basa bamba a nahiyar Afirka, ba kamar yadda aka saba ganin ana kyale tsoffin shuwagabanni ba, duk da irin tarin zarge zargen dake kansu na karkatar da kudaden al’umma a lokacin da suke mulki.

Zuma ya halarci Kotun ne sanye da bakar riga, inda aka hange shi yana daga ma magoya bayansa hannu a yayin da yake sanya kafa cikin Kotun da misalin karfe 8 na safiyar Juma’a, wanda hakan ke alanta Zuma na da sauran masoya a kasar, duk kuwa da irin zunuban da ake zargin ya tafka a baya.

A zaman Kotun, an girke jami’an Yansanda dauke da makamai zagaye da Kotun, don gudun karya doka daga dubunnan magoya bayan Zuma da suka halarci Kotun, a cewarsu bita da kulli ake masa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel