Nigerian news All categories All tags
Bashin dala miliyan 350: An samu rarrabuwan kawuna a tsakanin yan majalisun jihar Kaduna

Bashin dala miliyan 350: An samu rarrabuwan kawuna a tsakanin yan majalisun jihar Kaduna

Akalla yan majalisun jihar Kaduna guda shidda ne suka barranta da maganan da takwaransu, dan majalisa mai wakiltar mazabar Sabon gari a majalisar wakilan Najeriya, Datti Babawo yayi game da bukatar ciyo bashin dala miliyan 350 da gwamnatin jihar Kaduna ke so.

A yan kwanakin bayan ne dai majalisar dattawa tayi watsi da bukatar jihar Kaduna na ciyo wadannan makudan kudade biyo bayan rashin amincewa da bukatar da Sanatocin jihar, Shehu Sani, Hunkuyi da Danjuma Lar suka nuna.

KU KARANTA: Maganganun da Annabi Isa ya fada min a lokacin da ya bayyana a gareni har sau 4 – Inji wata Mata

Sai dai jim kadan bayan daukan wannan mataki na majalisar dattawa, dan majalisa Babawo Datti ya bayyana bacin ransa da haka, inda yace kafatanin yan majalisar wakilai, musamman wadanda suka fito daga jihar Kaduna su 15 sun yi amanna da ciyo bashin.

Abinka da siyasar ra’ayi, sai ga shi an samu wasu yan majalisu gida shida sun barranta da maganan Datti, inda suka ce Datti ba shi da hurumin yin magana da yawunsu, daga cikinsu akwai; Adams Jagaba, lucas Gwani, Simon Yakubu, Nicholas Shehu Garba, Sunday Marshal da kuma Muhammad Musa Sabo.

Yan majalisun sun karyata rahoton cewa Babawo ne shugabansu, haka zalika sun bayyana cewar basu taba tattauna batun ciyo bashin dala miliyan 350 a tsakaninsu ba, ballantana har su dauki mataki, daga karshe suka ce dukkanin majalisun dokokin Najeriya na zaman kansu ne, don haka basu ga dalilin da zai sa Datti ya caccaki matakin da majalisar dattawa ta dauka ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel