Nigerian news All categories All tags
Shugabanin addinin kiritsa sunki amincewa da tazarcen Buhari

Shugabanin addinin kiritsa sunki amincewa da tazarcen Buhari

Wata kungiyar shugabanin addinin Kirista 'United Christian Leaders Eagle Eye Forum' (UCLEEF) ta bayyana rashin amincewarta a akan kiraye-kiraye da wasu keyi na neman Shugaba Buhari ya sake tsayawa takara musamman gwamnonin jam'iyyar APC.

Sanarwan ta fito ne ta bakin shugaban kungiyar na kasa, Fasto Aminchi Habu, a wata taron manema labarai da ya kira bayan zaben sabbin yan kwamitin masu bayar da shawara na kungiyar a Abuja.

Habu yace gwamnatin APC bata tabukawa yan Najeriya komai ba musamman idan akayi la'akari da yadda ta kasa warware matsalar tsaro, rashin samar da ayyukan yi ga matasa da kuma karuwar talauci da rashin farfado ta tattalin arzikin Najeriya.

Shugabanin addinin kiritsa sunki amincewa da tazarcen Buhari

Shugabanin addinin kiritsa sunki amincewa da tazarcen Buhari

DUBA WANNAN: Kiwon lafiya: Magani 16 da shan ruwa da safe kafin cin komai ke yi

A cewarsa, lokaci yayi da shugabanin arewa da takwarorinsu na kudu zasu hada karfi da karfe don fitar da dan takara mai nagarta da zai karbe mulki daga gwamnati mai mulki a yanzu.

"Muna kira da manyan yan Najeriya kamar su Janar Yakubu Gowon (murabus), Janar Ibrahim Babangida (murabus), Janar Abdulsalami Abubakar (murabus) da Janar Aliyu Gusau (murabus) su hada kai don fitar da dan takara da yan Najeriya zasu amince dashi a zaben 2019.

"Farfesa Jerry Ghana, SenataIbrahim Mantu, Janar Theophilus Danjuma (murabus); Sarkin Zazzau, Dr. Shehu Idris; Kungiyar dattawan arewa (NEF); Kungiyar ACF da shugabanin matasan arewa da sauran yan Najeriya duk ya dace sun amsa wannan kira," inji Habu.

Ya kuma shawarci matasa su guji sayar da kuri'arsu don wani kudi kalilan da za'a basu saboda wani dan abin da ba'a rasa ba kamar yadda sukayi a baya kuma ya janyo wa kasar koma baya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel