Nigerian news All categories All tags
Babu kifin roba a Najeriya – Hukumar NAFDAC

Babu kifin roba a Najeriya – Hukumar NAFDAC

- Hukumar kula da kayan abinci (NAFDAC) tace bincikenta ya biyo bayan bincike data gudanar a dakin bincikenta akan wani kifi da ake zargin cewa na roba ne

- Tace binciken ya biyo bayan rahoto data samu daga wani mai amfani dashi a birnin tarayya wanda yace ya siya kifi amma yaki dahuwa

- Hukumar ta NAFDAC din tace kifin wanda take zargi bayan bincike data gudanar a kansa ta gane cewa wana dauke da wasu sinadarai a jikinsa wanda kuma kowane kifi nadasu

Hukumar kula da kayan abinci (NAFDAC), a ranar Alhamis, a birnin tarayya, tace bincikenta ya biyo bayan “bincike data gudanar a dakin bincikenta akan wani kifi da ake zargin cewa na roba ne”.

Hukumar tace: “binciken ya biyo bayan rahoto data samu daga wani mai amfani dashi a birnin tarayya wanda yace ya siya kifi amma yaki dahuwa bayan tsawon lokaci da akayi ana sa masa wuta”.

Hukumar ta NAFDAC din tace kifin wanda take zargi bayan bincike data gudanar a kansa ta gane cewa wana dauke da wasu sinadarai a jikinsa wanda kuma kowane kifi nadasu.

Babu kifin roba a Najeriya – Hukumar NAFDAC

Babu kifin roba a Najeriya – Hukumar NAFDAC

“Kifin an gane cewa bai kamata mutane su ringa amfani dashi ba saboda akwai wasu kwayoyin cuta a cikinsa, saboda haka ake bayyanawa mutane cewa ba wani kifin roba a Najeriya”.

KU KARANTA KUMA: Turkashi: Kungiyar Kato da Gora sun hana SARS kama Sanata Dino Melaye

Hukumar ta gargadi ‘yan Najeriya sau gaggauta kai rahoto ga Ofishinsu mafi kusa game da duk wani kayan abinci da basu aminta dashi, don a binciki lafiyarsa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel