Nigerian news All categories All tags
Lafiya jari: Za'a fara dashin koda a wannan asibitin koyarwar ta Najeriya

Lafiya jari: Za'a fara dashin koda a wannan asibitin koyarwar ta Najeriya

Mahukunta a babbar asibitin koyarwa ta jami'ar Najeriya dake a garin Enugu, babban birnin jihar Enugu dake a yankin kudu maso gabashin Najeriya sun bayyana cewa asibitin za ta fara yin tiyatar dashin koda ga marasa lafiya masu bukata.

Wannan dai, kamar yadda muka samu yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da asibitin ta fitar dauke da sa hannun kwararrun likitoci shidda a cikin satin da ya gabata.

Lafiya jari: Za'a fara dashin koda a wannan asibitin koyarwar ta Najeriya

Lafiya jari: Za'a fara dashin koda a wannan asibitin koyarwar ta Najeriya

KU KARANTA: Ko me Buhari zai je yi Landan?

Legit.ng ta samu kuma cewa hukumar asibitin ta zabtare kudin yin tiyatar daga kusan Naira miliyan 11 ya zuwa Naira miliyan 3 da rabi wanda a cewar su sun yi hakan ne domin samar da sauki ga masu bukarar hakan.

Haka ma dai hukumar gudanarwar asibitin ta zayyana cewa za su soma yin tiyatar ne a ranar 7 zuwa 14 ga watan Yulin da ke tafe don haka dukkan mai bukata sai ya garzaya asibitin domin karin bayani.

A wani labarin kuma, Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya ta Peoples Democratic Party, PDP tare da sauran magoya bayan ta sun bayyana shakkun su game da abunda suka kira dodoridon da fadar shugaban kasa ke yi wa 'yan Najeriya musamman ma game da tafiyar da yake shirin yi zuwa birnin Landan sati mai zuwa.

Haka ma dai jam'iyyar ta bukaci samun sahihin bayani game da lafiyar ta shugaban kasa da cikkanen abunda zai je yi tare da kuma adadin kudin kasa da zai kashe yayin tafiyar ta sa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel