Nigerian news All categories All tags
Cinikin makamai: 'Yan majalisar dattijai za su sake cakusawa da fadar shugaban kasa

Cinikin makamai: 'Yan majalisar dattijai za su sake cakusawa da fadar shugaban kasa

Alamu dai na kara nuna cewa da alama batun sayen makaman nan na makudan kudaden da suka kai Naira biliyan 360 da shugaba Buhari ya amince ayi da su za su kara kawo rikici tsakanin fadar shugaban kasar da kuma majalisar dattijai.

Wannan dai kamar yadda muka samu ya fara fitowa karara ne a ta bakin Sanata Ben Bruce da ke wakiltar mazabar jihar Bayelsa a zauren inda ya bayyana cewa Buhari bai da ikon sayen makaman har sai majalisar ta amince masa.

Cinikin makamai: 'Yan majalisar dattijai za su sake cakusawa da fadar shugaban kasa

Cinikin makamai: 'Yan majalisar dattijai za su sake cakusawa da fadar shugaban kasa

KU KARANTA: An kama wani kato ya boye 'yan mata 4 yana lalata da su a Kebbi

Legit.ng ta samu dai cewa dan majalisar ya bayyana hakan ne a yayin da yake fira da manema labarai.

Haka ma dai jam'iyyar adawa babba kuma tsohuwar jam'iyya mai mulki a Najeriya PDP ta zargi gwamnatin tarayya ta jam'iyyar APC karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari da shirya ma 'yan Najeriya gadar zare musamman ma game da kudin makaman da shugaba Buhari ya ware don sayen makamai.

Jam'iyyar ta PDP dai ta zargi cewa kudaden da suka kai Naira biliyan 360 jam'iyyar ta APC na shirin yin anfani ne da su domin gudanar da abubuwan da suka shafi ayyukan jam'yya da kuma kamfe din zabukan 2019.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel