Nigerian news All categories All tags
Rikicin Jam'iyyar APC yayi kamari har ta kai Shugaba Buhari ya daga tafiyar sa

Rikicin Jam'iyyar APC yayi kamari har ta kai Shugaba Buhari ya daga tafiyar sa

- Shugaba Buhari ba zai wuce Ingila ba sai bayan wani taron Jam’iyyar APC

- Jam’iyyar ta APC na neman sabawa shawarar da Shugaban kasar ya bada

- Buhari ya nemi ayi sabon zabe amma har yanzu APC ba ta da niyyar haka

Mun samu labari daga majiyoyi masu karfi cewa yanzu haka Shugaban kasa ya dakatar da tafiyar sa zuwa Landan ganin Likita har sai zuwa Ranar Litinin mai zuwa saboda rikicin da ya barke a Jam’iyyar APC mai mulki a halin yanzu.

Rikicin Jam'iyyar APC yayi kamari har ta kai Shugaba Buhari ya daga tafiyar sa

Wasu a Jam'iyyar APC na yunkurin barin Oyegun a kujerar sa

Shugaba Buhari zai tsaya taron Majalisar zartawa watau NEC na Jam’iyya domin ya tabbatar da cewa APC ta sa ranar yin zaben sababbin Shugabannin ta na kasa da Jihohi bayan da ya ji cewa wasu a Jam’iyyar na neman saba masa.

KU KARANTA: Gwamnoni 4 da ke kokarin ganin an kara wa'adin Oyegun

Masu neman ganin Shugaban Jam’iyyar John Oyegun ya zarce na kokarin amfani da Shugabannin Jam’iyyar APC na Jihohi wajen karawa John Oyegun wa’adi. Su ma dai Shugabannin Jihohin za su so su cigaba da zama a kujerun su.

Da alamu dai har yanzu Jam’iyyar ba ta da niyyar gudanar da zabe kamar yadda Shugaban kasa ya nema. An yi taro da Shugabannin Jihohi domin ganin Majalisar gudanarwa watau NWC ta amincewa Oyegun ya zarce a kujerar sa jiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel