Nigerian news All categories All tags
Wasu Sanatocin Najeriya sun yi awon-gaba da makudan kudi Dala $96000

Wasu Sanatocin Najeriya sun yi awon-gaba da makudan kudi Dala $96000

- A 2017 ne aka shirya horar da wasu 'Yan Majalisan Tarayyar Najeriya

- Hukumar da ta shirya horon a Kasar waje ta kuma zo ta fasa daga baya

- Duk da haka ana tunani 'Yan Majalisan sun karbe kudin wannan taron

Mun samu labari daga Jaridar Premium Times ta kasar nan ana zargin cewa wasu 'Yan Majalisan Tarayyar Najeriya sun karkatar da wasu makudan Dalolin kudi da aka shirya tura su zuwa Kasar waje domin wani horo a bara.

Wasu Sanatocin Najeriya sun yi awon-gaba da makudan kudi Dala $96000

Ana zargin 'Yan Majalisa da karkatar da wasu Daloli

Kwanakin baya Hukumar NBET ta kasar tayi niyyar fita da wasu 'Yan Majalisa zuwa Kasar waje sai dai kuma daga baya an fasa tafiyar. Sai dai duk da haka Majalisa ta warewa 'Ya 'yan na ta kudin da aka shirya na zirga-zirgar.

KU KARANTA: Ba na shan giya ko taba amma ina da son motoci - Dino Melaye

Duk da ba ayi wannan tafiya ba, ana zargin 'Yan Majalisun sun yi gaba da $96,350 wanda hakan ya sa masu suka ke ta suka a Kasar bayan da wasu majiyoyi su ka tabbatar da cewa an cire kudin daga asusun Majalisan Tarayyar kasar.

Wadannan 'Yan Majalisan Enyinnaya Abaribe, Adamu Alegria da sauran su. Haka kuma akwai wasu 'Yan Majalisar Wakilai da su ka hada da Hon. Muhammad Garba Gololo, Iboro Ekanem, Abdulmalik Zubairu da sauran su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel