Nigerian news All categories All tags
Zan Iya Fadawa Wuta Saboda Buhari, Zan Iya Yin Komai Akan Buhari - Gwamnan Kogi

Zan Iya Fadawa Wuta Saboda Buhari, Zan Iya Yin Komai Akan Buhari - Gwamnan Kogi

Gwamnan jahar Kogi Yahaya Bello, ya bayyana biyayyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da cewa zai iya fadawa wuta saboda Buhari.

Bello ya bayyana haka ne, yayin da yake bayyana matsayarsa kan matakin shugaban kasa kan shugabanci shugaban jam'iyyar APC na kasa John Oyegun.

Zan Iya Fadawa Wuta Saboda Buhari, Zan Iya Yin Komai Akan Buhari - Gwamnan Kogi

Buhari da gwamna Yahaya Bello

Ya ce, "Ni dan gani-kashe-nin Muhammadu Buhari ne, kuma shi yace dole mu bi abinda ke cikin kundin tsarin mulkin kasar nan na 1999 da kuma kundin tsarin jam'iyyar mu ta APC. Da Buhari zai ce min na fada cikin wuta, wallahi da gudu zan afka ciki."

DUBA WANNAN: Kisan dan mamba a majalisar wakilan Najeriya: Hukumar 'yan sanda ta saka ladan miliyan N8m

Da aka tambaye shi cewa me yasa da farko ya goyi bayan karin zangon mulki ga shugaban jam'iyya John Oyegun? Sai ya kada baki yace,

"Mutane na cewa wai adawa nake da Asiwaju Bola Tinubu; wai shi yasa na goyi bayan karin zangon shugabanci. Ina so ku sani bani da matsala da Asiwaju, shugaba na ne. Buhari kuma shine shugaban mu duka. A baya kam na goyi bayan Oyegun." In ji gwamnan jahar Kogi Yahaya Bello

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel