Nigerian news All categories All tags
Kisan dan mamba a majalisar wakilan Najeriya: Hukumar 'yan sanda ta saka ladan miliyan N8m

Kisan dan mamba a majalisar wakilan Najeriya: Hukumar 'yan sanda ta saka ladan miliyan N8m

- Hukumar 'yan sanda a birnin Landan ta saka ladan Fam €20,000 kwatankwacin miliyan N8m ga duk wanda ya bayar da muhimmin bayani a kan kisan Abraham Badru

- An kashe matashin ne ranar 26 ga watan Maris a Hackney dake birnin London a kasar Ingila

- Abraham, mai shekaru 26, shine mutum na 10 da aka kashe a kasar Ingila cikin kwanaki 12

An kashe matashi Abraham Badru, da ga dan majalisar wakilan Najeriya, Dolapo Badru, ranar 26 ga watan Maris a Hackney dake birnin Landan a kasar Ingila.

Rahotanni sun bayyana cewar an kashe Abraham; mai shekaru 26, yayin da ya bude bayan motar sa domin daukar wani abu bayan ya dawo gida.

Kisan dan mamba a majalisar wakilan Najeriya: Hukumar 'yan sanda ta saka ladan miliyan N8m

Marigayi Abraham Badru

Abraham ya taba samun kyautar jarumta daga jami'an tsaro a kasar Ingila bayan ya kwaci wata matashiya da wasu karti suka yi kokarin yiwa fyade.

Abraham, kocin kungiyar kwallon kafa, shine mutum na goma da aka kashe cikin kwanaki 12 a birnin Landan.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga a kasar Ingila sun harbe dan mamba a majalisar wakilan Najeriya

Yanzu haka hukumar 'yan sanda a birnin Landan ta bayyana cewar zata bayar da ladan Fam 20,000, kwatankwacin Naira miliyan N8m ga duk wanda ya samar da muhimman bayanai da zasu kai ga gano wanda ya kashe Abraham.

Abraham, da ne ga dan majalisar wakilai mai wakiltar Lagos Island, Dolapo Badru.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel