Nigerian news All categories All tags
Da duminsa: Dagachi da wasu mutane biyar sun mutu a wani sabon hari a Kaduna

Da duminsa: Dagachi da wasu mutane biyar sun mutu a wani sabon hari a Kaduna

A yau, Alhamis, ne da rana wasu 'yan bindiga suka kai hari kauyen Sarari dake garin Kuriga a karamar hukumar Birnin Gwari tare da kashe Dagacin garin da wasu mutane biyar.

An kai harin ne da misalin karfe 2:00 na ranar yau.

Wani daga cikin wadanda suka samu rauni yayin harin, Henry, ya tabbatar da mutuwar Dagachin kauyen nasu.

Ya ce 'yan bindigar sun dira garin ne a kan babura tare da bi gida-gida suna harbin jama'a.

Da duminsa: Dagachi da wasu mutane biyar sun mutu a wani sabon hari a Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna; Nasir El-Rufa'i

Jaridar premium times ta rawaito cewar dukkan mutanen da suka mutu maza ne, kuma babu yaro a cikinsu.

DUBA WANNAN: Tayar da tarzoma: An garkame mutane 63 a gidan yari a jihar Kaduna

Henry ya bayyana cewar sunan Dagachin garin nasu da aka kashe; Sule Sarari, mai shekaru 60 a duniya. Ragowar sune; Lado, Yunusa, Jonah, Tela da wani mutum guda.

An kai gawar mutanen asibitin garin Oduwa mai nisan wasu takaitattun kilomita daga kauyen da aka kai harin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel