Nigerian news All categories All tags
Fiye da ma'aikata 20,000 muka dauka cikin shekaru 3 domin don ƙarfafa dakarun Soji - Mansur Dan Ali

Fiye da ma'aikata 20,000 muka dauka cikin shekaru 3 domin don ƙarfafa dakarun Soji - Mansur Dan Ali

Ministan tsaro na kasa Birgediya Janar Mansur Dan Ali, ya bayyana cewa hukumar tsaro karkashin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ƙarfafa tare da ingantuwa a sakamakon fiye da ma'aikata 20, 000 da ta dauka.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, hukumar Sojin da dauki ma'aikata fiye da 20, 000 cikin shekaru uku da suka gabata a sassa daban-daban na dakarun sojin kasa, sama da kuma na ruwa.

A ranar da ta gabata ne ministan ya bayyana hakan ne a yayin bikin yaye dalibai 195 na sabbin shiga soja da aka gudanar a jihar Kaduna.

Ministan Tsaro; Mansur Dan Ali

Ministan Tsaro; Mansur Dan Ali

Ministan ya bayyana cewa, hobbasan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi na amincewa da Dala biliyan 1 wajen sayen makamai zai taimaka kwarai da aniyya wajen yakar rashin tsaro da kasar nan ke fama shekaru aru-aru.

KARANTA KUMA: Kungiyar Musulman Lauyoyi ta ki amincewa da sabuwar dokar Kotu kan tsarin sanya Tufafi

Da yake jawabi a yayin bikin yaye daliban, Dan Ali ya umarci sabbin sojin 195 da suka samu horo na tsawon watanni shida da su tabbatar da kare mutuncin kasa da kuma aiki tukuru wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu kamar yadda kundin tsarin mulki ya gindaya.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, an rufe fiye da masallatai da Coci 6000 a kasar Rwanda sakamakon rashin hali na kulawa da su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel