Nigerian news All categories All tags
An fallasa badakalar da sakataran APC da wasu gwamnoni ke shiryawa

An fallasa badakalar da sakataran APC da wasu gwamnoni ke shiryawa

- Sirrin boye ya fito fili, An gano shirin wasu gwamnoni na kitso da kwarkwata

- Gwamnonin basa so Buhari yayi tafiya ba tare da an cimma matsaya ba

A cigaba da lalubo hanyar da zasu bi wurin tilasatawa jam’iayyar APC aiwatar da zaben shugabannin ta na kasa, kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi da ayi.

Wasu daga cikin gwamnonin jam’iyyar ta APC na can sun dukufa wajen kitsa zaren yadda za’a canza tsarin da jam’iyyar ke bi, ta hanyar canza kwanan watan wasikar gayyatar da za'a aikewa da mambobin kwamitin zartarwa na jam’iyyar domin halartar taron gaggawa kamar yadda majiyar Premium Times ta rawaito.

Yanzu-yanzu: An fallasa badakalar da sakataran APC da wasu gwamnoni ke shiryawa

Mala Buni

Gwamnonin dai na yunkurin tilastawa sakataren jam’iayyar na kasa, Mala Buni sauya kwanan watan katin gayyatar taron gaggawa da za’a gudanar ranar Litinin 9 ga watan afrilu.

Bayan taron da aka gudanar ne na ranar Laraba, gwamnonin su kayi kira ga Shugabannin jam’iyyar da suyi amfani da shawarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar na sake sabon zabe maimakon karin wa’adi da kai.

Duk kuwa da cewa kwamitin da jam’iyyar ta kafa da zai bata shawarwari don fitar da Jaki daga duma, karkashin shugabancin gwamnan Jihar Plateau, Simon Lalong bai kammala bincikensa ba.

Yanzu-yanzu: An fallasa badakalar da sakataran APC da wasu gwamnoni ke shiryawa

Simon Lalong

Wasu daga cikin yan jam’iyyar APC sun bayyana cewa, ba dai-dai ba ne yunkuri da ake don kuwa maganar na gaban kwamiti, kuma tsarin mulkin jam’iyyar ya hana daukar duk wani mataki matukar maganar na gaban kwamiti, kamar yadda sashi na 18 na kundin tsarin mulkin jam'iyyar ya tanadar.

Gwamnonin dai na aniyar sha gaban rahoton da kwamitin da aka kafa don nemo mafita ga al’amarin dake faruwa.

KU KARANTA: 2019: Adawar da IBB da Obasanjo ke nunawa ba siyasa bace

"Bayan da aka yi musu bayanin abinda wannan sashin na kundin tsarin mulkin yake cewa, sai suka yanke shawarar bullo da wani sabon salo, na kiran taron gaggawa. domin bukatar gwamnonin it ace, su gaggauta gudanar da taron kafin hutun da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke shirin tafiya birnin London daga ranar Litinin 9 ga wata." A cewar majiyar Jaridar ta Premium Times.

Ba sa son a jinkirta daukar wani mataki sai bayan tafiyar Buhari, shi ne suke gaggawar gudanar da taron majalisar zartarwar kafin ya tafi hotun.

“Sashin da gwamnonin suka fi damuwa da shi, shi ne sashi na 25B(ii), wanda yake bayanin yadda za’a iya shirya taron gaggawa na majalisar zartarwa idan bukatar hakan ta taso, domin dole ne a aika da katin gayyata a kalla kwanaki bakwai ga mambobin kwamitin kafin gudanar da taron.” A cewar majiyar.

Yanzu-yanzu: An fallasa badakalar da sakataran APC da wasu gwamnoni ke shiryawa

APC LOGO

Majiyar ta cigaba da cewa, ganin ba zasu iya cimma wannan kudiri nasu ba sakamakon kurewar lokaci ne yasa gwamnonin suka nemi sakataren jam’iyyar na kasa, Mala Buni da ya canza kwanan watan katin gayyatar daga 4 zuwa 3 watan Afrilu, alhalin an rubuta takardar ne a ranar 4 ga wata, domin kuwa har ya zuwa karfe takwas na daren (8pm) jiya ba a rubutawa. Majiyar ta tabbatar.

Amma sai dai Mala Bunin yaki amincewa da wannan bukatar ta su sakamakon tsoro da yake na abinda ka iya zuwa ya koma.

Sakataren yasan tabbas cewa ko a cikin gwamnonin wani na iya tona asirin abinda ya faru” Inji majiyar Premium Times da yammcin ranar Laraba.

Har ya zuwa karfe tara da minti bakwai (9:07 a.m) na safiyar yau alhamis, wani Sanata da kuma yake cikin mambobin kwamitin majalisar zartarwar jam’iyyar, ya tabbatar da cewa bai amshi wata gayyata zuwa taron da za’a gudanar ranar Litinin din ba.

Sanatan ya ce shi dai yana da labarin cewa, da akwai shirin aikawa da katin gayyatar ta sakon waya (Text), amma har yanzu bai ga wani katin gayyata ko sakon waya ba. A bayanin majiyar ga jaridar Premium Times.

Duk wani yunkurin da akai na tuntubar, Sanata Sani Yerima daga Jihar Zamfara, wanda shi ma mamba ne na kwamitin, bai cimama nasara ba, sakamakon kin amincewa ya yi magana akan batun.

Yanzu-yanzu: An fallasa badakalar da sakataran APC da wasu gwamnoni ke shiryawa

Sanata Sani Ahmed Yarima

Mutukar wannan yunkuri na gwamnonin ya samu nasara, hakan ya tabbatar sun aikata ba daidai ba, maimakon dinke baraka da suke kokarin yi.

Majiyar ta ce tana dari-darin watakila sakataren jam’iayyar Mala Bunu na iya fuskantar tursasawa har ya amince da wannan bukata tasu.

“Tabbas ba za mu zuba ido muna gani shuwagabannin da suka yi alkawarin kawo gyaru su rika aikata ba dai-dai ba, wanda akarshe shugaban kasa Muhammadu Buhari zasu bari da jangwam, sakamakon son ran su da suka aikata.” A cewar wani jigo a jam’iyyar ta APC da ya bukaci a buye sunansa.

Amma sai dai duk da irin wannan dambarwa da ke faruwa, kakakin jam'iyyar na kasa, Bolaji Abdullahi ya ce, “Ba ni da wata masaniya cewa sakataren Jam’iyyar yana fuskantar wata tursasawa don ya canza kwanan watan wasikar gayyata zuwa taron gaggawar.” Sai dai ku tambaye shi da kansa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel