Nigerian news All categories All tags
Yadda 'yan fashi suka kai hari tare da yin awon gaba da mata uku daga cikin masu bauta a wata Cocin Abuja

Yadda 'yan fashi suka kai hari tare da yin awon gaba da mata uku daga cikin masu bauta a wata Cocin Abuja

Wasu gungun 'yan fashi da makami sun kai hari wata Coci, New Ona Iwa Mimo Onimajemu Cherubim and Seraphim, dake unguwar Kwaso a yankin Tudun-Maje dake Zuba a garin Abuja.

Babban limamin Cocin, Oladejo John, ya sanar da manema labarai cewar, 'yan fashi sun yi harbe-harben iska domin firgita jama'a kafin daga bisani su yi awon gaba da kudade da wayoyi da wasu mata guda uku.

Rahotanni sun bayyana cewar, 'yan fashin, su hudu, na sanye da kakin soji sannan sun rufe fuskokinsu.

An kai harin ne da misalin karfe 2:00 na daren ranar Talata kuma 'yan fashi sun sace wasu mata uku da suka zo Cocin domin gudanar da addu'o'in dare.

Yadda 'yan fashi suka kai hari tare da yin awon gaba da mata uku daga cikin masu bauta a wata Cocin Abuja

Wata Cocin Katolika

Limamin Cocin ya ce, a lokacin da 'yan fashin ke kokarin tafiya da matan guda hudu ne sai ya jefa kwalba, fashewar kwalbar ya saka 'yan fashin tunanin harbin bindiga ne har ta kai ga sun harba ta su bindigar tare da guduwa su bar daya daga cikin matan a harabar Cocin.

Wata mata, Bose Komolafe, da abin ya faru kan idonta ta shaidawa manema labarai cewar, barayin sun umarci kowa ya kwanta ya kifa fuskar sa kasa, sannan sai suka tambayi inda Faston Cocin yake.

DUBA WANNAN: Tayar da tarzoma: An garkame mutane 63 a gidan yari a jihar Kaduna

Bayan Fasto ya mike ya nuna kansa, sai suka tambaye shi inda yake ajiye bindigar sa da kudin Coci.

Bose ta kara da cewar, sun daki Faston kafin su kwace kudade da wayoyin jama'ar dake Cocin sannan suka yi awon gaba da mata hudu hudu daga cikin masu bauta a Cocin.

Yanzu haka 'yan fashin sun tafi da mata uku bayan sun saki daya daga cikinsu tare da shaidawa Faston cewar ba zasu sako matan ba sai ya biya kudin fansa, miliyan N5m.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar da safiyar aka shigar da korafin faruwar lamarin ofishin 'yan sanda na zuba kuma tuni suka fara binciken al'amarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel