Nigerian news All categories All tags
Matasan Jam’iyyar APC sun yi kaca-kaca da Dattawan Arewa

Matasan Jam’iyyar APC sun yi kaca-kaca da Dattawan Arewa

- Wasu Matasan APC sun ce a 2019 ne za su yi wa barayin kasar nan ritaya

- Wani ‘Dan APC yace Dattawan Arewa su ne ke raba kan al’ummar kasar

- A cewar sa ‘Yan Arewa sun fi amfana da aikin da Gwamnati ke yi a Kudu

Mu na da labari cewa wani Matashi wanda yana cikin manya a Jam’iyyar APC mai mulki Auwal Hassan yayi kaca-kaca da Dattawan Arewa a wata hira da yayi a gidan Talabijin na Channels TV.

Matasan Jam’iyyar APC sun yi kaca-kaca da Dattawan Arewa

Mu na tare da Shugaba Buhari inji Matasan APC

Auwal Hassan wanda Matashi ne ya bayyana cewa Dattawan Arewa su ne matsalar Yankin da ma kasar inda ya bayyana cewa da su aka rika yi wa Muhammadu Buhari adawa ana murde masa zabe tun 2003 har Ubangiji ya sa yayi nasara a 2015.

KU KARANTA: Fastocin Arewa sun ziyarci Shugaban kasa Buhari

Hassan ya nuna cewa Jigon APC a Kasar Yarbawa Bola Tinubu ne ya hada kai da Shugaba Buhari wanda hakan ya ba shi nasarar lashe zabe a 2015 don haka babu dalilin korafi don Shugaban kasar yayi a aiki a Yankin Yarbawa domin haka siyasa ta gada.

Matashin ya nuna cewa ‘Yan Arewa su ka fi kowa amfana da hanyar Legas zuwa Ibadan da ake yi da kuma titin jirgin da za ayi daga Legas zuwa Kano. Hassan yace a zaben 2019 Matasa za su yi amfani da Shugaba Buhari su tika Dattawan da kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel