Nigerian news All categories All tags
Yan majalisa 9 sun mutu cikin shekara 3 – Me ke faruwa ne?

Yan majalisa 9 sun mutu cikin shekara 3 – Me ke faruwa ne?

Cikin shekaru 3 na majalisan dokokin tarayya na takwas, an yi rashin mutane 9 daga cikinsu yawanci ba tare da rashin lafiya ko jinya ba.

Ga jerin wadanda suka riga mu gidan gaskiya cikin yan majalisa:

1.Ahmed Zanna,

An zabe shi a matsayin mai wakiltar Borno ta tsakiya a majalisan dattawa, amma ya rasu a watan Afrilun 2015 kafin ma a rantsar da shi.

2. Isiaka Adeleke,

Sanata mai wakiltan Osun ta yamma, ya rasu da safiyar Lahadi, 23 ga watan Afrilu, 2017 a asibitin Biket ba tare da wani jinya ba.

3. Ali Wakili

Sanata mai wakiltan Bauchi ta kudu, ya rasu ne ranan 16 ga watan Afrilu 2018 da safiyar Asabar ba tare da wani jinya ba.

KU KARANTA: Buhari ya karbi bakuncin Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Ahmad

4. Mustapha Bukar

Mustapha Bukar, sanata mai wakiltan Katsina ta Arewa ya rasu jiya Laraba, wannan shine mutuwa na 9 a majalisan dokokin tarayya cikin shekara 3.

5. Umar Buba Jibril,

Dan majalisa mai wakiltan mazabar Lokoja ya rasu ne ranan Juma’a, 30 ga watan Maris, 2018 bayan jinya.

6. Elijah Adewale,

Dan majalisa mai wakiltan mazabar Ifako Ijaiye na jihar Legas, ya mutu ne a ranan Alhamis, 21 ga watan Yuli 2016 ba tare da wani jinya ba.

7. Abdullahi Wammako,

Dan majalisa daga jihr Sokoto, ya rasu ne ranan 14 ga watan Yulin 2017 bayan gajeruwar jinya.

8. Musa Baba-Onwana

Dan majalisa mai wakiltan Nasarawa/Toto na jihar Nasarawa. Ya rasu ranan 17 ga watan Maris 2017. Babu wanda ya san sanadin mutuwarsa.

9. Bello Sani

Dan majalisa mai wakiltan Mashi/Dvisi na jihar Katsina, ya rasu ranan 15 ga watan Fabrairu, 2017.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a: https://facebook.com/naijcomhausa https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel