Nigerian news All categories All tags
Tattalin arzikin Najeriya yafi samun kulawa karkashin Jonathan fiye da Buhari - PDP

Tattalin arzikin Najeriya yafi samun kulawa karkashin Jonathan fiye da Buhari - PDP

- Jam’iyyar PDP tayi ikirarin cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan yafi Shugaban kasa Muhammadu Buhari kula da tattalin arzikin Najeriya

- Mataimakin ciyaman na jam’iyyar PDP, Yemi Akinwonmi, yayi wannan ikirari bayan nadin Adebutu da matarsa a matsayin Otunba Badekale

- Ya bukaci ‘yan Najeriya da suyi kokarin sauke gwamnatin APC daga mulki a zaben 2019, saboda matsatsin da janyowa ‘yan kasa da rashi kula da tattalin arzikin kasa

Jam’iyyar PDP tayi ikirarin cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan yafi Shugaban kasa Muhammadu Buhari kula da tattalin arzikin Najeriya.

Mataimakin ciyaman na jam’iyyar PDP, Yemi Akinwonmi, yayi wannan ikirari bayan nadin Adebutu da matarsa a matsayin Otunba Badekale na Makun, Sagamu da Yeye Otunba shima a matsayin Badekale, Sagamu, wanda Ewusi na Badekale, Sagamu, a karkashin Oba Timothy Akinsanya.

Ya bukaci ‘yan Najeriya da suyi kokarin sauke gwamnatin APC daga mulki a zaben 2019, saboda matsatsin da janyowa ‘yan kasa da rashi kula da tattalin arzikin kasa. Yace tunda mutane sun dandana mulkin jam’iyyun biyu yanzu sun gane cewa gara mulkin PDP dana APC.

Yace sakamakon wahalar da akesha na rayuwa yanzu a Najeriya dole mu komawa PDP don samun mafita.

Tattalin arzikin Najeriya yafi samun kulawa karkashin Jonathan fiye da Buhari - PDP

Tattalin arzikin Najeriya yafi samun kulawa karkashin Jonathan fiye da Buhari - PDP

Yace “Mutane yanzu sun dandana kowane mulki na jam’iyyun biyu sun gane wanda yafi, tinda bamu taba shiga irin wannan halin ba a Najeriya. Bamu da lokacin sauraren ‘yan adawa gurinmu kawai shine muci zabe”.

KU KARANTA KUMA: Zogala: Maganin dake kashe cutar daji ya kuma hana cutar siga

Akinwonmi yace a lokacin PDP $1 idan ka canza zaka samu N180 lokacin mulkin Shugaba Jonathan, amma yanzu kaga $1 ta kai N360, yace wannan gwamnatin bata san yanda zatayi ta farfado da tattalin arzikin kasar nan ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel