Nigerian news All categories All tags
'Yan shi'a sun lashi takobin cigaba da zaman dirshan a titunan Abuja duk da farmakin da 'Yan sanda suka musu

'Yan shi'a sun lashi takobin cigaba da zaman dirshan a titunan Abuja duk da farmakin da 'Yan sanda suka musu

Wata kungiya mai fafutikan dabbaka demokradiya, bin doka da yaki da rashawa mai suna 'Concerned Nigerians' tayi Allah-wadai da harin da Yan sanda suka kai wa mambobin ta tare da 'Yan Shia (IMN) yayin da suke zanga-zangar lumana a Unity Fountain da ke Abuja.

A sanarwan da ta fito daga bakin Sakataren yadda labarai na kungiyar, Theophilus Abu Agada, ya bayyana cewa 'Yan sanda sun far wa yan kungiyar tare da sauran masu gudanar da zanga-zangar lumana inda suka bukatar gwamnati ta saki Sheikh Ibrahim Elzakzaky wanda aka tsare fiye da kwanaki 800.

Tsare El-Zakzaky: Wata kungiya tayi alwashin cigaba da zaman dirshan duk da barazanar da 'yan sanda keyi musu

Tsare El-Zakzaky: Wata kungiya tayi alwashin cigaba da zaman dirshan duk da barazanar da 'yan sanda keyi musu

DUBA WANNAN: An mayar da Janga a matsayinsa na kwamishinan 'Yan sanda a jihar Kogi

"Muna matukar damuwa yadda yanzu muke rayuwa a kasar da al'umma basu da damar bayyana ra'ayinsu ko kuma gudanar da zanga-zangar lumana ba tare da yan Sandan daya kamata su karesu sun ci mutuncinsu ba.

"Dole ne hukumar Yan sanda ta dena danne mana hakkin da dokar kasa ta bayar na gudanar da taro cikin zaman lafiya. Kungiyar mu ba na masu tayar da hankali bane kuma sun ranar da muka fara zaman dirshan na kin amincewa da tsare Zakzaky bamuyi wani tashin hankali ba.

"Dole ne a kawo karshen irin wannan cin mutunci da zarafin da akeyi wa al'ummar Najeriya," inji kungiyar.

Kungiyar ta dau alwashin cigaba da zaman dirshan din a kullum har sai an biya diyyar wadanda aka kashe ba tare da wani hakki ba a Zaria kuma an sako Shugaban Shia na Najeriya Sheikh Ibrahim Elzakzaky tare da matar sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel