Nigerian news All categories All tags
A kalla mutane 3,000 ne suka koma gidajensu bayan an bude hanyoyin Maiduguri-Bama-Banki

A kalla mutane 3,000 ne suka koma gidajensu bayan an bude hanyoyin Maiduguri-Bama-Banki

- Kungiyar kula da masu gudun hijira (IOM) ta kasashen duniya, tace gwamnatin Najeriya ta mayar da mutane a kalla 3,000 ‘yan garin Bama gidajensu

- Tace an mayar dasu gidajensu ne bayan an bude hanyar Maiduguri-Bama-Banki shekaru hudu bayan da aka rufeta saboda Boko Haram

- IOM tace mayar da ‘yan gudun hijirar zuwa gidajensu ya kara yawan wadanda keda bukatar tallafin gwamnati

Kungiyar kula da masu gudun hijira (IOM), ta kasashen duniya, tace gwamnatin Najeriya, ta mayar da mutane a kalla 3,000 ‘yan garin Bama, a jihar Borno zuwa gidajensu.

IOM tace an mayar dasu gidajensu ne bayan an bude hanyar Maiduguri-Bama-Banki, a ranar 24 ga watan Maris, shekaru hudu bayan da hukumar Sojin Najeriya ta rufeta saboda Boko Haram.

IOM tace mayar da ‘yan gudun hijirar zuwa gidajensu ya kara yawan wadanda keda bukatar tallafin gwamnati.

A kalla mutane 3,000 ne suka koma gidajensu bayan an bude hanyoyin Maiduguri-Bama-Banki

A kalla mutane 3,000 ne suka koma gidajensu bayan an bude hanyoyin Maiduguri-Bama-Banki

Hanyar wadda ta taso daga Maiduguri ta biyo ta Konduga, Bama, Gwoza, har ta hade da kasashe ketare wanda suka hada da Cameroon da Chad, wadda aka rufe a watan Satumba shekarar 2014.

KU KARANTA KUMA: Alamu 7 da mutum zai gane jikinsa na bukatar ruwa wanda mutane basu sani ba

Kungiyar tace anga motoci sama da 200 dauke da mutane daga Bama wasu kuma na tafiya Baman.

Ta kara da cewa gwamnatin Najeriya ta aika da kayan abinci da kananan injina na wuta da abubuwa da dama zuwa garin Bama, don ta karawa mutane karfin gwiwar komawa garin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel