Nigerian news All categories All tags
Za a dakatar da Daliban da aka kama da laifin satar jarrabawa na tsawon shekaru

Za a dakatar da Daliban da aka kama da laifin satar jarrabawa na tsawon shekaru

- Hukumar jarrabawar yammacin Afirika (WAEC) tace daliban da aka kama da laifin satar jarabawa baza'a barsu su sake rubuta wata jarabawar ba har na tsawon wasu shekaru. Wannan hukuncin yana daya daga cikin abubuwan da suka zartar a taron da suka gudanar a jihar Legas a karkashin kwamitin jarabawa taa Najeriya

Za a dakatar da Daliban da aka kama da laifin satar jarrabawa na tsawon shekaru

Za a dakatar da Daliban da aka kama da laifin satar jarrabawa na tsawon shekaru

Hukumar jarrabawar yammacin Afirika (WAEC) tace daliban da aka kama da laifin satar jarabawa baza'a barsu su sake rubuta wata jarabawar ba har na tsawon wasu shekaru. Wannan hukuncin yana daya daga cikin abubuwan da suka zartar a taron da suka gudanar a jihar Legas a karkashin kwamitin jarabawa taa Najeriya.

DUBA WANNAN: Wani sabon maganin zazzabin cizon sauro dake maida jinin mutum guba ga sauro

Kamar yanda shugaban kwamitin Demianus Ojijieogu ya sa hannu, kwamitin ta yanke hukunce-hukunce ga duka wasu hanyoyin satar jarabawa. Bayan kwamitin ya gama sauraron korafe korafe na satar jarabawar, kwamitin yayi cikakken bincike inda ya bayyana wasu hukunce-hukuncen akan laifukan satar jarabawar kamar yanda dokokin jarabawar ya tanada.

Dokar da kwamitin ta kafa tace, "ta bada goyon bayan soke jarrabawar duk wani dalibin da aka kama da laifin satar amsa, da kuma soke dukkan darussan da aka kama dalibi yana satar jarabawar akai. Ya kara da cewa wasu daliban za a ladaftar dasu ne ta hanyar dakatar dasu daga rubuta jarabawar na tsawon wasu shekaru. Hukuncin da kwamitin ta yanke zai biyo bayan tabbatar da shi ba tare da bata lokaci ba, sannan za a sanar da daliban da abin ya shafa da kuma cibiyoyin rubuta jarabawar. Kwamitin ta kara da cewa zata saki sakamakon daliban da aka tabbatar da babu sa hannun su a satar Jarabawar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel