Kungiyar Musulman Lauyoyi ta ki amincewa da sabuwar dokar Kotu kan tsarin sanya Tufafi

Kungiyar Musulman Lauyoyi ta ki amincewa da sabuwar dokar Kotu kan tsarin sanya Tufafi

Kungiyar Musulman Lauyoyi ta Najeriya watau MULAN (,Muslim Lawyers' Association of Nigeria) ta ki amincewa da sabuwar doka da babbar kotun kasa dake birnin tarayya ta gindaya kan tsarin yadda lauyoyi za su rinka yin shiga ta tufafi.

A cewar kungiyar, babbar Kotun a wata sanarwa ta ranar 28 ga watan Maris na shekarar 2018, ta hana duk wata shiga da lauyoyi za su sanya wani tufafi karkashin hular su ta aiki, wanda ga dukkan alamu suke hani da sanyan hijabi da Lauyoyin mata suka saba.

Kungiyar Musulman Lauyoyi ta ki amincewa da sabuwar dokar Kotu kan tsarin sanya Tufafi

Kungiyar Musulman Lauyoyi ta ki amincewa da sabuwar dokar Kotu kan tsarin sanya Tufafi

Sai dai a cikin wata sanarwa da kungiyar ta gabatar a karshe taron shugabannin ta da ta gudanar na ranar 3 ga watan Afrilu a birnin Benin na jihar Edo, kungiyar ta hau kujerar naki tare da bayyana rashin amincewar ta kan wannan doka da cewar muzgunawa ce gami da rashin adalci ga musulmai.

A cikin sanarwar da sanadin shugabanta Dakta Kamak Dawud ya bayyana cewa, umarnin da babbar Kotun ta gindaya ya sabawa sashe na 38 cikin kundin tsarin mulki kasa da ya baiwa al'umma 'yancin gudanar da ra'ayoyin su na addini.

KARANTA KUMA: Wani Matashi ya gurfana gaban Kuliya da laifin fyade diyar makwabci a jihar Legas

Ya kara da cewa, umarnin Kotun ya sabawa dokar kungiyar Lauyoyi da ta baiwa Lauyoyin mata dama ta sanya hijabi karkashin hular su ta Lauyoyi.

A yayin haka kuma jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, gwamnonin APC 20 sun bukaci kafa kwamitin tsara gangamin jam'iyyar da za a gudanar a watan Yuni.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel