Nigerian news All categories All tags
An kashe wata mata an kuma sace mata jaririya 'yar wata shida

An kashe wata mata an kuma sace mata jaririya 'yar wata shida

- Wadanda ake zargin masu safarar yara kanana sun sace jaririya ‘yar wata shida da haihuwa bayan sun kashe mahaifiyarta

- Matar mai shekaru 28 ta bata ne tun ranar 22 ga watan Maris 2018, amma an gano gawarta a cikin wani rami a ranar 24 ga watan Maris

- A lokacin da daya daga cikin masa satar yaran ke kokarin jefa gawar cikin rami mutanen gari sun ganshi amma kafin a kira jami’an tsaro ya gudu

Wadanda ake zargin masu safarar yara kanana sun sace jariya ‘yar wata shida da haihuwa bayan sun kashe mahaifiyarta, mai suna Helen Ehianu, a kauyen Obior, a karamar hukumar Aniocha dake jihar Delta.

An kashe wata mata an kuma sace mata jariri 'yar wata shida

An kashe wata mata an kuma sace mata jariri 'yar wata shida

Matar mai shekaru 28 ta bata ne tun ranar 22 ga watan Maris 2018, amma an gano gawarta a cikin wani rami a ranar 24 ga want Maris.

DUBA WANNAN: Kuyi watsi da 'yan adawa masu bakar aniya: Fadar shugaban kasa ta shawarci 'yan Najeriya

Jaridar Punch Metro ta ruwaito cewa, lokacin da daya daga cikin ‘yan ta’addan ke kokarin jefa gawar cikin rami mutanen gari sun ganshi amma kafin mutane su taru, a kira jami’an tsaro ya gudu.

Dan uwan marigayiyar mai suna Samuel Ehianu, yace kawar marigayiyar mai suna Precious tanada hannu a kisan ‘yar uwarsa, saboda a ranar 22 ga watan Maris Precious ta dauke ta daga gidansu dake Ekwuoma, a gabas maso arewacin Ika zasu Ogwashi don neman maganin farfadiya.

Samuel yace mutanen unguwar da aka samu gawar ‘yar uwar tasa sunce sunji wata kara daga gidan wanda suke zargi yana da hannu a kisan ‘yar uwar tasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel